"Matsalar Lafiya" Amarya Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci Wata 2 da Aure

"Matsalar Lafiya" Amarya Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci Wata 2 da Aure

  • Wata amarya mai suna, Salamat Suleiman, ta nemi saki a Kotun Ilorin, babban birnin jihar Oyo saboda matsalar lafiyar mijinta
  • Matar ta shaida wa Alkali cewa mijinta na da tsinkakken ruwan kwayar halinta kuma ta gaji da hakurin zama da shi
  • A ɓangarensa magidanci ya amince da abinda matarsa ta faɗa amma ya nemi Kotu ta ba shi lokaci domin ya lalubo bakin zaren

Oyo - Wata matar Aure mai suna Salamat Suleiman, ta shigar ƙarar neman saki a gaban Kotu bayan wata biyu da ɗaura mata aure bisa hujjar Angonta bai da cikakkiyar lafiya.

Amaryar watanni biyun ta shaida wa Kotu cewa bayan aurensu ta fahimci cewa ruwan kwayar halittar mijinta a tsinke yake, watau ba shi da kauri kamar yadda aka sani.

Nema saki a Kotu.
"Matsalar Lafiya" Amarya Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci Wata 2 da Aure Hoto: vanguard
Asali: UGC

Salamat da roki Kotun mai zama a Ilorin, babban birnin jihar Ilorin, ta raba auren domin ta gaji da zaman hakuri da mijin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa Ta Magantu Kan Kalaman Da Mijinta Ya Yi, Ta Ce Kalaman Ba Gaskiya Ba Ne

Shin mijin ya amince da abinda matar ta faɗa a Kotu?

Da yake nasa jawabin, wanda ake ƙara kuma angon Salamat ya amince cewa yana fama da rashin lafiya, amma ya jaddada cewa itama matar tana da matsalar lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa har yanzun yana ƙaunar matarsa kuma ya roƙi Kotu ta taimaka ta ba shi lokaci domin warware saɓanin da ya shiga tsakaninsu.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Alkalin Kotun, mai shari'a Abdul Qadir Umar, ya shaida wa matar cewa kada ta tsaya boye-ɓoye, su garzaya wurin likita su nemi maganin wannan matsala.

Haka nan kuma Alkalin ya shawarci Amarya ta ƙara bai wa Angonta dama a karo na biyu, kuma ya gaya mata cewa duk wani aure yana da kalar na shi kalubalen.

Rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa Kotu ta ɗage zaman zuwa ranar 28 ga watan Augusta, 2023, inda zata saurari rahoton sulhun ma'auratan da kuma yuwuwar ci gaba da sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An yi ram da wasu mazauna Qatar, rikakkun 'yan safarar kwaya a wata jiha

Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa

A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya shiga ƙunci bayan Likita ya shawarce shi da matarsa kar su kusanci juna na tsawon kwanaki 7 watau mako ɗaya.

A wani bidiyo da matar ta wallafa a soshiyal midiya, kwararren likitan ya shawarci mutumin ya haƙura na ɗan wani lokacin kafin ya kwanta da matarsa amma ya nuan ba zata saɓu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262