Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

  • Muhammadu Sanusi II ya sa labule da Shugaban Najeriya, kuma ya fadi abin da su ka tattauna a kai
  • Khalifan ya ji dadin yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tunkari matsalar tattalin arzikin kasa
  • Sanusi II ya kuma bukaci ayi bincike a kan yadda sojoji su ka hallaka wasu makiyaya a Nasarawa

Abuja - Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya yabi Bola Ahmed Tinubu a dalilin karfin halin da ya yi wajen janye tsarin tallafin man fetur.

This Day ta ce Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya kuma jinjinawa Shugaban kasa bayan da ya yi fatali da bambanci wajen farashin kudin ketare.

Sanusi II ya bayyana matsayarsa ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya hadu da Mai girma shugaban kasa a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gajerun Bayanai a Kan Mutane 8 Da Tinubu Ya Nada a Matsayin Masu Bada Shawara

Tsohon Sarkin Kano
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II Hoto: www.unsdgadvocates.org
Asali: UGC

Tsohon Sarkin ya bayyana Bola Tinubu a matsayin abokinsa wanda ya ce ya kama hanyar gyara kasa, ya ce a dalilin hakan ne ya kawo masa ziyara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dalilin farko shi ne in zo in taya shi murna a hukumance. Sannan kuma da yake ina dauke da huluna da-dama, ina sanye da hular masanin tattali saboda haka na zo in gode masa a kan matakan da ya dauka domin farfado da tattalin arzikin nan.
Kuma kamar yadda aka san abubuwan da mu ke magana a kai: tallafin man fetur ya zama ala-ka-kai, bambancin farashin kudin kasar waje da sauransu.
Wadannan su ne abubuwan da ni na ke magana a kai na tsawon lokaci, kuma na yi farin ciki da a ranar farkonsa ya tabo su, ‘yan kasuwa su na murna."

- Muhammadu Sanusi II

An rahoto Sanusi II yana cewa ya na dakyau idan gwamnati tayi abin yabo to a fada, a maimakon ya zama ba a cewa uffan sai suka idan an yi kuskure.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Jami’an Gwamnati 1 Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Cikin Makonni 2

"Saboda haka ya fara da kyau, idan ana maganar tattalin arziki ne, an fara da kafar dama. Mun zo ne domin mu mara masa baya, kuma mu karfefe shi.
Bola Tinubu ya cigaba a wannan hanya, kuma ya tsaya a kan manufofin da yake kai."

- - Muhammadu Sanusi II

Khalifan Tijjaniyan ya ce ya kawo maganar kashe makiyaya 37 da sojojin sama su ka yi a jihar Nasarawa, ya bukaci gwamnatin tarayya tayi bincike.

Sanusi II ya ce ya na so gwamnati ta magance sabanin da ke tsakanin makiyaya da manoma.

Wa za a ba Ministoci?

Ana da labari maganar neman kujerun Ministoci ya kara karfi bayan shugaban kasa ya nada Nuhu Ribadu da wasu masu bada shawarwara na musamman.

Alal misali akwai ‘yan takara birjik da ke neman mukamai a Delta, Zamfara da duk inda APC ta rasa. Mutane sun zura ido domin jin wa za a dauko a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel