Bola Tinubu Ya Nada Masu Bada Shawara, ‘Yan APC Sun Fara Hangen Kujerun Ministoci

Bola Tinubu Ya Nada Masu Bada Shawara, ‘Yan APC Sun Fara Hangen Kujerun Ministoci

  • Ana sauraron wadanda Bola Tinubu zai zama su rike masa kujerun Ministocin tarayya a gwamnatinsa
  • Tsofaffin Gwamnoni, jagororin jam’iyya da ‘yan takara duk su na so shugaban kasar ya ba su mukamai
  • Akwai Jihohin da Tinubu zai rasa daga ina zai kama, daga Kano akwai mutane da-dama da ake kawowa

Abuja - Rassoshin jam’iyyar APC na jihohi, su na sauraron Bola Ahmed Tinubu ya bukaci su aika masa jerin wadanda su ke so a ba kujerun Ministoci.

Punch ta kawo rahoto a ranar Juma’a cewa tsofaffin gwamnoni, jiga-jigan jam’iyya, tsofaffin Ministoci da wasu makamantansu su na harin mukamai.

Ana tunanin Shugaba Bola Tinubu zai sha wahala wajen dauko Minstocin da zai yi aiki da su daga jihohin Zamfara, Filato, Delta da musamman Kano.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya na gaisawa da Gwamna Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Tinubu ya ce za a iya damawa da kowa

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Shigo da Sabuwar Doka, Ana Sa Ran Mutane 500, 000 Za Su Samu Aiki

Akwai jihohin da jam’iyyar APC ta rasa kujerun Sanatoci da Gwamnoni, rahoton ya ce hakan zai jawowa Tinubu ciwon kai idan ya tashi kafa gwamnati.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin da ake sa ran Shugaban na Najeriya ya zabo wadanda su ka san aiki domin ya ji dadin mulki, ana bukatar ya tuna da wadanda su ka fadi zabe.

Mai girma Shugaban kasar ya taba nuna zai tafi da kowa a mulkinsa, ya ce ba za a rasa inda za a cusa duk ‘yan jam’iyya da sauran mutanen Najeriya ba.

Faduwa zabe ya canza lamari a APC

Daga Delta, ana ganin ya kamata a sake ba Festus Keyamo kujerar Minista, sai dai rashin nasarar Sanata Ovie Omo-Agege a zaben Gwamna ya dagula lissafi.

Da farko ana tunanin Farfesa Isaac Adewole zai koma kujerarsa, amma hukuncin kotun koli a kan zaben Osun ya sa an koma maganar Gboyega Oyetola.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan CBN: Tsohon Gwamna, Masu Bankuna Da Wasu Kwararru Da Ke Sa Ran Gaje Kujerar Emefiele

Sanata Ibrahim Gobir bai samu tikitin takarar Gwamnan Sokoto ba, don haka wasu su ke ganin shi ya dace da Ministan musamman tun da bai bar APC ba.

Jam’iyyar APC ta rasa Kano don haka ‘yan takara da-dama su na hangen gwamnatin sama, ana tunanin Abdullahi Ganduje ya kwallafa rai a kujerar Minista.

Maganar da ake yi, jagororin APC a Zamfara sun dage wajen ganin an ba su mukamai masu tsoka. Bello Matawalle da Kabir Marafa sun ba APC gudumuwa.

Tinubu ya nada Hadimai 8

Rahoto ya zo cewa Shugaban Najeriya ya dauko wasu kwararru da za su rika ba shi shawarwari na musamman a mulki, daga cikinsu akwai Nuhu Ribadu.

Bola Tinubu ya dauko mutum biyu daga Gwamnatin Muhammadu Buhari, ya ba su mukamai a gwamnatinsa, ya kuma zabo kwamishinar Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel