Mataimakan Gwamnan CBN 4 Da Za Su Iya Gadon Kujerar Godwin Emefiele

Mataimakan Gwamnan CBN 4 Da Za Su Iya Gadon Kujerar Godwin Emefiele

  • A ranar Juma’a 9 ga watan Yuni Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan Babban Bankin Kasa CBN, Godwin Emefiele
  • Godwin Emefiele ya kasance gwamnan babban bankin CBN tun a watan Maris na shekarar 2014 da tsohon shugaban kasa Goodluck ya nada shi
  • Ana zargin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele da badakalar makudan kudade lokacin da ya ke kan kujerar shugabancin bankin

A ranar Talata 6 ga watan Disamba ta shekarar 2022, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika sunayen Edward Adamu da Aisha Ahmed ga majalisa don tantance su a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin Najerya (CBN).

Bukatar sake zaben nasu a wannan matsayi ya kasance shi ne na biyu kuma na karshe a wancan lokaci, cewar Legit.ng.

Mataimakan gwamnan CBN 4 da ake sa ran za su gaji kujerar Emefiele
Mataimakan Gwamnan CBN. Hoto: CBN
Asali: UGC

A shekarar 2018 Buhari ya amince da nadin Edward Adamu a matsayin mataimakin gwamnan CBN.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele: Wike Ya Yi Martani Ga Hukuncin Tinubu Na Dakatar Da Gwamnan CBN

A shekarar 2016 Edward Adamu ya zama darakta ta bangaren ma’aikata kafin daga bisani ya zama mataimakin gwamnan CBN.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabancin gwamnan CBN na karewa bayan wa’adi biyu akan kujera, daga nan za a dauko wani daga cikin manyan ma’aikatan bankiwadanda ba sa aiki a CBN.

Tsohon gwamnan CBN da aka dakatar, Godwin Emefiele ya kasance Babban Daraktan bankin Zenith, kafin daga bisani tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya nada shi a matsayin gwamnan CBN a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 2014.

Datatar da Emefiele da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Juma’a 9 ga watan Yuni bai ba wa mutane mamaki ba saboda sanin cewa Tinubu ba zai bari ya dade ba, cewar TheCable.

Manyan mataimakan gwamnan CBN sun hada da:

1. Aishah N. Ahmad

An nada Aisha Ahmed a matsayin mataimakiyar gwamnan CBN a watan Maris na shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Matakin da Shugaba Tinubu Ya Ɗauka Na Dakatar da Gwamnan CBN

Ta jagoranci bangaren kudade don inganta wannan bangare, kuma ta na daga cikin kwamitin gudanarwa na CBN.

Aisha ta yi aiki a bankunan NAL da bankin Zenith da kuma bankin Stanbic IBTC.

2. Edward L. Adamu

Edward Adamu ya zama mataimakin gwamnan CBN a watan Maris na shekarar 2018.

Adamu ya gama karatun digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 1981.

Ya halarci kwasa-kwasai da dama da suka shafi gudanarwa don inganta harkokin rayuwarsa, da kuma karin karatu bayan kammala digiri dinsa.

3. Folashodun Adebisi Shonubi

Folashodun Adebisi Shonubi shi ne mataimakin gwamnan CBN ta bangaren gudanar da ayyuka na bankin.

Ya kammala digiri na biyu a bangaren gudanar da kasuwanci a jami’ar Lagos.

Shonubi ya yi aiki a wurare da dama a bankuna na kasar, ya rike daraktan bangaren bayanai da sadarwa a hukumar tsaro ta Renaissance.

Ya kuma yi aiki a bankin FCMB a matsayin mataimakin shugaba, da kuma babban daraktan a bankin Ecobank, sannan ya yi aiki na kankanin lokaci a bankin Citibank ta bangaren adana hannun jari.

Kara karanta wannan

Bayanai 5 Game da Injiniyan da Zai Zama Gwamnan CBN Bayan Dakatar da Emefiele

4. Kingsley Obiora

Kingsley Obiora ya fara aiki a matsayin mataimakin gwamnan CBN a ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2020.

Ya yi aiki a matsayin babban darakta na hukumar IMF a birnin Washington, sannan ya kasance mai ba da shawara na musamman akan harkar tattalin arziki na gwamnan CBN.

Ya kammala digiri dinsa na farko a jami’ar Benin da digiri na biyu da kuma na uku a jami’ar Ibadan.

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

A wani labarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Willie Bassey ya sanyawa hannu daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Juma'a 9 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel