Godwin Emefiele: Wike Ya Jinjinawa Tinubu Kan Dakatar Da Emefiele a Matsayin Gwamnan CBN

Godwin Emefiele: Wike Ya Jinjinawa Tinubu Kan Dakatar Da Emefiele a Matsayin Gwamnan CBN

  • Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana ra'ayinsa kan dakatar da Godwin Emefiele da Tinubu ya yi a matsayin gwamnan CBN
  • Jigon na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hukuncin a matsayin ci gaba mai kyau
  • Ya yaba ma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan daukar wannan tsatsauran hukunci na dakatar da Emefiele

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jinjinawa shugaban kasa Bola Tinubu kan dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Ku tuna cewa Legit.ng ta rahoto labarin dakatar da Emefiele a daren ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Bola Tinubu,Godwin Emefiele da Nyesom Wike
Godwin Emefiele: Wike Ya Jinjinawa Tinubu Kan Dakatar Da Emefiele a Matsayin Gwamnan CBN Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Twitter

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ne ya sanar da labarin dakatar da Emefiele din a cikin wata sanarwa da ya fitar.

An kuma yi umurnin cewa Emefiele ya mika harkokin babban bankin kasar ga mataimakin gwamna, Folashodun Shonubi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya nuna yana da alkibla, Wike kan dakatar da Emefiele

Da yake martani ga ci gaban, Wike, daya daga cikin mutanen da suka soki manufofin Emefiele, musamman sauya fasalin naira, ya bayyana matakin da shugaban kasar ya dauka a matsayin wanda ya dace kuma kan lokaci.

Channels TV ta rahoto cewa tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma yaba ma shugaban kasa Tinubu kan amincewa da shekarun ritaya da fansho na ma'aikatan shari'a a kasar, a cewar wata sanarwa da tawagar labaransa suka fitar.

Ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka zai haifar da wani sabon rayuwa ga bangaren shari’a na kasar.

Wike ya bayyana cewa shi da mambobin G5 sun ji dadin cewa shugaban kasar yana nuna cewa yana da alkibla da shugabanci abun koyi wanda zai kawo ci gaba a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel