"CBN Ya Tallafa Masa": Dalibin Sakandire Ya Zana N200 da Fensir Mai Kaloli

"CBN Ya Tallafa Masa": Dalibin Sakandire Ya Zana N200 da Fensir Mai Kaloli

  • Wani ɗalibin sakandire a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, ya yi amfani da alƙalamin rubutun yara Fensir ya zana takardar N200
  • Ɗalibin mai hazaƙa da aka bayyana sunansa da Abraham Magu, ya ja hankalin soshiyal midiya saboda ƙayataccen zanen da ya yi
  • Wasu daga cikin masu ta'amali da soshiyal midiya sun yaba da ƙwazon yaron yayin da wasu suka buƙaci a ɗauki nauyin karatunsa

Wani ɗalibin makarantar Sakandire mai hazaƙa ya yi amfani da kaloli daban- daban na alkalamin rubutun yara Fensir ya zana takardar kuɗi N200.

Dalibin, wanda aka bayyana sunansa da Abraham Magu, ya yi wannan ƙwazo na zanen takardar N200 a wani hoto da yanzu haka ya ja hankalin mutane a shafin Facebook.

Magu.
"CBN Ya Tallafa Masa": Dalibin Sakandire Ya Zana N200 da Fensir Mai Kaloli Hoto: AT Clenzy Funny Zone
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa Magu yana karatu ne a Makarantar Sakandiren Mount Saint Gabriels Secondary School (MSG), Makurdi, babban birnin jihar Benuwai a Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Takardar naira N200 da yaron ya zana da Fensir ta yi matuƙar kyau ta yadda wasu mutane ke ganin ta fi wacce babban bankin Najeriya (CBN) ya buga ake amfani da ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗalibin ya watsu a soshiyal midiya saboda zanen N200

Magu, ya nuna basira wajen zana hoton Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato daidai kuma cikin salo da ƙwarewa ya fito da dukkan kalolin da aka sani a jikin naira 200.

Duk wani abu da ke jikin N200 ta asali, Magu ya sanya shi a cikin zanensa kuma gwanintar da ya nuna ce ta sa ya karɓu a wurin jama'a.

Zuwa yau 8 ga watan Yuni, 2023, mutane da dama sun sake wallafa Hoton zanen da Magu ya yi a shafin daga ciki har da AT Clenzy Funny Zone.

Martanin mutane kan batun

Kara karanta wannan

Daga Karshe Wike Ya Bayyana Gaskiya Kan Batun Yi Wa Tinubu Magudin Zabe a Jihar Rivers

Nwabueze Okolie ya ce:

"Kaddara zata kaika inda baka tunani, karka ja da baya, ka ci gaba da abinda kake ganin ya dace, ina son haka."

Pst Olaleye Bode ya ce:

"Ya kamata CBN ya ɗauki nauyin karatunsa, bayan ya kammala ya ba shi gurbin aiki."

Monday Omorowa ya ce:

"Ya kamata shugaba Tinubu ya ɗauki wannan yaron a haɗa shi da gwamnan CBN nan gaba idan za'a canja fasalin taƙardun kuɗi."

Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

A wani labarin kuma Wani matashi ya koka bayan wata budurwa ta damfare shi sannan ta goge shi ta yadda ba zai iya tuntuɓarta ba har abada.

Ya ce shi ya fara mata magana da nufin su san juna amma daga bayan kyakkyawar budurwar ta bar shi da cizon yatsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel