Wike Ya Musanta Yin Magudi a Zaben Shugaba a Jihar Rivers Saboda Shugaba Tinubu

Wike Ya Musanta Yin Magudi a Zaben Shugaba a Jihar Rivers Saboda Shugaba Tinubu

  • Nyesom Wike ya yi fatali da rahotannin da ke cewa ya yi maguɗin zaɓe a zaɓen shugaban ƙasan Najeriya na 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya musanta zargin yin maguɗi a zaɓen domin shugaba Bola Tinubu ya yi nasara a jihar Rivers
  • Rahotannin bincike da dama daga manyan jaridu biyu ya nuna cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, shi ne ya lashe zaɓe a jihar

Jihar Rivers - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewa bai yi dana sanin abubuwan da ya yi ba lokacin da ya ke mulkin jihar mai arziƙin man fetur.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da BBC Pidgin, kan inda ya dosa a siyasa tun bayan barinsa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Wike ya musanta yin magudin zabe a jihar Rivers
Wike ya ce kotu za ta gano gaskiya Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike CON/Facebook da @officialABAT/Twitter
Asali: UGC

Lokacin da ake tattaunawar an yi masa tambaya kan zargi da binciken da jaridun BBC da Premium Times suka gudanar wanda ya nuna an yi maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa a jihar saboda shugaba Tinubu na jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan ya haƙiƙance cewa babu maguɗin zaɓen da aka yi a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Babu wani maguɗin zaɓen da aka yi a zaɓen shugaban ƙasa." A cewarsa.
"Lamarin yana gaban kotu, yanzu ya rage kotu ta gano wanda ya tafka maguɗin zaɓe da wanda bai aikata ba."

Sakamakon binciken BBC da Premium Times

Tun da farko dai binciken da BBC ta gudanar ya tabbatar da cewa an sauya sakamakon zaɓen jihar Rivers domin ba shugaba Tinubu nasara.

Rahoton ya tabbatar da cewa ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, shi ne ya yi nasara a zaɓen da tazara mai nisa.

Rahoton na BBC na cewa:

"Mun gano an yi wa Tinubu aringizon ƙuri'u 106,000 a sakamakon zaɓen da aka bayyana lokacin da muka kwatanta shi da abinda muka samu a rumfunan zaɓe, wanda hakan ya kusa ninka yawan ƙuri'un da ya samu a jihar."

Haka kuma wani rahoton binciken Premium Times ya tabbatar da Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Rivers.

Bola Tinubu Ya Fada Mani Wanda Yake So Ya Zama Shugaban Majalisa

A wani labarin na daban kuma, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gaya masa wanda yake so ya zama shugaban majalisa.

Sanatan na jihar Borno ya bayyana cewa Sanata Godswill Akpabio shi ne ɗan takarar shugaba Tinubu a kujerar shugabancin majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel