"Ba Wayau": Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

"Ba Wayau": Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

  • Wani matashi ya koka bayan wata budurwa ta damfare shi sannan ta goge shi ta yadda ba zai iya tuntuɓarta ba
  • A cikin wata hira da aka fitar, budurwar mai suna Chiwendu ta tura masa lambar asusun ajiya a banki domin ya turo mata kuɗin mota
  • Sai dai bayan ya tura mata kuɗin motar, sai ta goge shi kawai ta yadda ba zai iya tuntuɓarta ba kwata-kwata

Wani matashin ɗan Najeriya ya nuna takaicinsa bayan wata kyakkyawar budurwa ta yi masa shigo-shigo ba zurfi.

Ya tuntuɓeta inda ya nemi da su haɗa su tattauna domin su san juna, inda bata yi musu ba ta yarda da hakan.

Matashi ya koka bayan budurwa ta damfare shi
Ta guje shi bayan ya tura mata kudi Hoto: @Bryan Julius
Asali: UGC

Ta tura masa lambar asusun ajiyarta na banki inda nan da nan cikin tsuma da ɗoki ya tura mata kuɗi ba tare da sanin cewa zai yi nadamar hakan ba.

Jim kaɗan bayan ya tura mata kuɗin, kawai sai ta daina ɗaukar kiransa a waya inda daga ƙarshe kuma ta goge shi ta yadda ba zai iya ƙara sake ji daga gareta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke wallafa hirar su a Facebook, matashin mai suna Bryan Julius ya bayyana cewa:

"Duk lokacin da na yi tunanin cewa na samu masoyiya sai a damfare ni. Har yanzu ina neman so na gaskiya. Wacce za ta nuna min so wacce za mu kasance da juna."

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani bayan budurwa ta damfari wani matashi

Cat Blade ya rubuta:

"Soyayya duk ƙarya ce."

Promise Mgba ya rubuta:

"Meyasa ka kyaleta hakanan?"

Mercy Ufomba ta rubuta:

"Har nawa ne ka tura mata?"

Beauty Victor ta rubuta:

"Na tausaya ma ka sosai."

Chinedu Edinho ya rubuta:

"Ka bi a hankali duk irin waɗannan ƴan matan tatse maka aljihu kawai za su yi."

Matashi Mai Samun N100k Ya Bukaci Budurwa Mai Samun N34m Ta Aje Aikinta Ta Aure Shi

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya je wajen budirwae da ya ke son ya aura da wata buƙata mai ban mamaki.

Matashin ya buƙace budurwar mai samun kuɗin da suka fi na shi yawa da ta ajiye aikinta domin su yi aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel