Rashin Daraja: DJ Ya Addabi 'Yan Islamiyya da Kida Ya Gamu da Fushin Alkali

Rashin Daraja: DJ Ya Addabi 'Yan Islamiyya da Kida Ya Gamu da Fushin Alkali

  • An gurfanar da wani matashi Mai kayan sauti a kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano saboda damun makarantar Islamiyya
  • Wanda ake zargin Ali Dan-Asabe yana kawo cikas ga daliban makarantar Islamiyya wanda ke hana su sauraran abin da malamansu ke koya musu
  • Alkalin kotun, Munzali Idris Gwadabe ya umarci tsare wanda ake zargin da kuma dage sauraran karar zuwa 6 ga watan Yuli don ci gaba karar

Jihar Kano – Kotun Shari’ar Mususlunci da ke zamanta a jihar Kano ta ajiye wani mai kayan sauti Ali Dan-Asabe bisa zarginsa damun makarantar Islamiyya a yankin.

Kotun wadda ke Dambare a karamar hukumar Ungogo ta tuhumi mai kayan kidan ne saboda yana kawo cikas ga Islamiyyar wurin hana karatun yara tafiya yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: Magidanci Da Matarsa Ta Yi Kararsa Ya Ki Halartar Zaman Kotu Saboda Kudin Mota a Kaduna

Kotu ta tsare wani mai kayan sauti kan damun dalibai a islamiyya a Kano
Kotu a Najeriya. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

An gurfanar da Ali Dan-Asabe a gaban kotun bayan samun korafi daga hukumar makarantar kan cewa karar kidan nasa yana kawo cikas ga daliban makarantar da kuma dauke musu hankali akan karatunsu.

Yadda mai kayan sautin ke hana daliban makarantar Islamiyya sauraran karatu

Mai gabatar da kara, Sifeta Bashir Wada ya fada wa kotu cewa karar abin kidan na Dan-Asabe yana hana yaran sauraron abin da malamansu ke koya musa a cikin aji, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan ana zarginsa da kunna kidan da ya sabawa al’adu da kuma tsarin mutanen jihar.

A cewarsa:

“Lokacin da hukumar makarantar ta same shi akan lamarin, Ali ya ce ba zai rage karar sautin kayan kidan ba, madadin haka sai ya kara sautin kayan kidan nasa.”

Rahotanni sun tattaro cewa wanda ake zargin tuni ya amince da zargin nasa da ake yi.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Al'umma a Arewa, Sun Kashe Mutane Masu Yawan Gaske

Alkalin kotun ya umarci a tsare wanda ake zargin tare da dage sauraran karar

Alkalin kotun, Munzali Idris Gwadabe ya umarci a tsare Ali da kuma dage sauraran karar zuwa ranar 6 ga watan Yuli don ci gaba da shari’ar.

Magidanci Da Matarsa Ta Yi Kararsa Ya Ki Halartar Zaman Kotu Saboda Kudin Mota a Kaduna

A wani labarin, wani mutum da ake zargi a kotu ya gaza halartar zaman kotun saboda rashin kudin mota.

Wanda ake zargin, Ali Abubakar ya bayyana wa kotun a waya cewa ba shi da kudin motar zuwa Kaduna don halartar zaman kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel