'Yan Bindigan Da Suka Sace Babban Basarake a Abuja Sun Nemi N9m a Matsayin Kudin Fansa
- Bayan shafe kwanaki a hannunsu, ƴan bindiga sun kira waya domin neman kuɗin fansar basaraken da suka sace a birnin tarayya Abuja
- Ƴan bindigan sun nemi da a biya su kuɗin fansa har N9m na dagacin ƙauyen Ketti da kuma wasu mutum biyu da suka haɗa da su
- Hadimin basaraken shine ya tabbatar da neman kuɗin fansan da ƴan bindigan suka yi bayan sun tuntuɓi iyalansa
Abuja - Miyagun ƴan bindigan da suka sace dagacin ƙauyen Ketti a ƙaramar hukumar Abuja Municipal (AMAC), Cif Sunday Zakwoyi, da wani hadiminsa, Markus Gade, sun nemi kuɗin fansa.
Ƴan bindigan waɗanda suka haɗa da kuma a wani mazaunin ƙauyen a lokacin farmakin, sun buƙaci da a basu N9m a matsayin kuɗin fansa, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Asali: UGC
Rahotanni sun tabbatar da cewa da safiyar ranar Juma'a da ta gabata, ƴan bindigan suka dira a fadar basaraken sannan suka yi awon gaba da shi tare da hadiminsa da wani mutum ɗaya.
Ƴan bindigan sun kira waya
Wani hadimin basaraken wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya bayyana a ranar Talata cewa shugagan ƴan bindigan ya kira waya a ranar Lahadi, ta hannun wayar ɗaya daga mutanen da suka sace.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hadimin ya bayyana cewa shugaban ƴan bindigan ya tuntuɓi ɗaya daga cikin iyalan basaraken inda ya buƙaci da a biya N3m kan kowane mutum ɗaya da suka sace waɗanda ke tsare a hannunsu.
Har ya zuwa yanzu dai, kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh, bata yi ƙarin haske ba akan lamarin.
Ƴan bindiga a cikin ƴan kwanakin nan suna matsawa yankunan da ke a birnin tarayya Abuja, inda suke shiga suna cin karensu babu babbaka, tare da yin awon gaba da mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Yan Bindiga Sun Sace Mutum Hudu a Birnin Tarayya Abuja
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutum huɗu a birnin tarayya Abuja.
Ƴan bindigan sun dira ne a yankin Mpabe na Abuja inda suka riƙa bin gida-gida sna tasa ƙeyar mutanen da suka zo ɗauka.
Asali: Legit.ng