INEC Ta Saki Jerin Sunayen 'Yan Takarar Gwamna a Jihohin Kogi, Bayelsa Da Imo

INEC Ta Saki Jerin Sunayen 'Yan Takarar Gwamna a Jihohin Kogi, Bayelsa Da Imo

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta saki jerin sunayen ƙarshe na ƴan takarar gwamnan jihohin Kogi, Bayelsa da Imo
  • Kwamishinan INEC na ƙasa, Festus Okoye ya ce jerin ya ƙunshi jam'iyyu 18 a jihar Kogi, 17 a jihar Bayelsa da 16 a jihar Imo
  • Okoye ya kuma tunatar da jam'iyyu da ƴan takararsu da su gudanar da yaƙin neman zaɓe mai tsafta ba tare da hargitsi ba

FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, (INEC) a ranar Talata, 6 ga watan Yuni, ta saki jerin sunayen ƙarshe na ƴan takarar zaɓen gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa, Kogi da Imo.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Festus Okoye, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe: Cikakken Jerin Jihohin Da Peter Obi Ke Kalubalantar Sakamakon INEC

INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar gwamna na jihohin Kogi, Bayelsa da Imo
INEC a ranar Talata ta saki jerin sunayen 'yan takarar gwamnan jihohin Bayelsa, Kogi da Imo Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Ya bayyana amincewa da jerin sunayen ya biyo bayan zaman da hukumar ta yi ne a ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

An ɗora jerin sunayen ƴan takarar gwamnan a shafin yanar gizo na INEC

Okoye ya ƙara da cewa an sanya jerin sunayen a shafin yanar gizo na hukumar da kuma shafukanta na soshiyal midiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Okoye, za a sanya sunayen kuma a ofisoshin hukumar na jiha da ƙananan hukumomin da jihohin da abin ya shafa a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni kafin wa'adin ranar ƙarshe na Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Zaben gwamna a jihohin Kogi, Bayelsa, Imo: Adadin yawan ƴan takara

Sanarwar ta INEC ta nuna cewa jam'iyyu 18 sun zaɓi ƴan takara a jihar Kogi, 17 a jihar Bayelsa da 16 a jihar Imo.

Jerin sunayen ya nuna cewa a jihar Bayelsa, jam'iyyu biyu suna da ƴan takara mata, yayin da a jihar Kogi jam'iyya ɗaya ta ke da ƴar takara mace. A jihar Imo babu ƴar takara mace ko guda daya.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Hukumar ta kuma yi nuni ga jam'iyyun siyasa da ƴan takararsu cewa za a fara yaƙin neman zaɓe ne a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, kamar yadda jadawalin abubuwan da za a yi ya nuna. Lokacin yaƙin neman zaɓe zai ƙare ne a ranar 9 ga watan Nuwamban 2023.

Okoye ya kuma buƙaci jam'iyyu da ƴan takararsu da su gudanar da yaƙin neman zaɓensu cikin tsafta ba tare da takalar faɗa ba.

A Karshe INEC Ta Bayyana Ainihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna

A wani labarin na daban kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta fito fili ta bayyana wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kaduna.

Hukumar shirya zaɓen ta bayyana cewa Malam Uba Sani na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), shi ne ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel