'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Hudu a Birnin Tarayya Abuja

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum Hudu a Birnin Tarayya Abuja

  • Ƴan bindiga sun sake kai farmaki birnin tarayya Abuja da sanyin safiyar ranar Asabar inda suka tasa ƙeyar mutum huɗu
  • Ƴan bindigan sun shiga unguwar Mashafa ne ɗauke da miyagun bindigu sannan suka wuce kai tsaye gidajen waɗanda suka zo ɗauka
  • Wani mazaunin unguwar ya shaida cewa ƴan bindigan musamman suka zo domin ɗauke mutanen da suka sace

Abuja - Ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai a safiyar ranar Asabar, sun farmaki unguwar Mashafa a cikin Mpape a birnin tarayya Abuja.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa, ƴan bindiga sun yi awon da gaba da mutum huɗu, a farmakin da suka kai unguwar wanda suka shafe kusan sa'a ɗaya.

Yan bindiga sun sace mutum hudu a Abuja
'Yan bindigan sun rika shiga gidaje suna tafiya da mutanen Hoto: Guardian.com
Asali: UGC

Wani mazaunin unguwar mai suna Zack ya bayyana cewa miyagun ƴan bindigan sun zo ne musamman saboda wasu ƴan unguwar.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutum 2 a Birnin Tarayya Abuja

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun riƙa shiga gidajen waɗanda suka zo nema ne daban-daban, inda suka tafi da su da ƙarfin tsiya, rahoton The Times ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun yo shiri ne musamman domin ɗauke wasu mutane

A kalamansa:

"Da sanyin safiya suka zo ɗauke da miyagun bindigogi. Bindigun su suna da ƙara sosai kuma sun kwashe kusan sa'a ɗaya. Mutanen da suka sace ya nuna cewa dama can domin su suka zo."
"Ɗaya bayan ɗaya suka riƙa bin su gidajensu suna ɗauke su da ƙarfin tuwo. Akwai shugaban wani kamfani, manajan gidan biredi, manajan gidan mai da wani wanda ya ke aiki a kamfanin gine-gine.

Ko da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta yi alƙawarin za ta bayar da bayanai nan gaba. Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a samu ji daga gareta ba.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Datti Baba-Ahmed Ya Dau Zafi, Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutum 2 a Abuja

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani basarake a birnin tarayya Abuja, a tsakar daren ranar Alhamis.

Ƴan bindigan sun kuma haɗa da wasu mutum biyu sun yi awon gaba da su a ƙauyen Ketti cikin ƙaramar hukumar Abuja Municipal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel