Daga Karshe Kotu Ta Yankewa Fasto Hukuncin Kisa Bayan Kashe Mawakiyar Coci

Daga Karshe Kotu Ta Yankewa Fasto Hukuncin Kisa Bayan Kashe Mawakiyar Coci

  • An yankewa wani faston Najeriya, Chidiebere Okoroafor, hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kisan mutane a jihar Ribas
  • An hukunta Okoroafor kan kisan wata mawakiya a cocinsa, Orlunma Nwagba, da kawarta, Chigozie Ezenwa, da diyarta mai watanni 11, Cresabel, a 2017
  • An yi zargin cewa malamin addinin ya yi wa mawakiyar cocin ciki kafin ya kashe ta a karamar hukumar Oyigbo da ke jihar Ribas

Port Harcourt, Jihar Rivers - An yankewa shugaban cocin Altar of Solution and Healing Assembly, da ke Oyigbo, jihar Rivers, Chidiebere Okoroafor, hukuncin kisan kai ta hanyar rataya.

A cewar jaridar The Punch, Okoroafor na fuskantar shari'a kan kisan wata mawakiyar cocinsa, Orlunma Nwagba, wacce ake zargin ya yi wa ciki da kashe kawar Orlunma, Chigozie Ezenwa, da diyarta mai watanni 11, Cresabel, a ranar 11 ga watan Disambar 2017.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Fasto a taron manema labarai
Daga Karshe Kotu Ta Yankewa Fasto Hukuncin Kisa Bayan Kashe Mawakiyar Coci Hoto: Ololade Olabanji Olamide Osanyintuyi
Asali: Facebook

A hukuncinsa, Justis S.O Benson na babbar kotu da ke zama a Port Harcourt, ya yi umurnin cewa a kashe Okoroafor ta hanyar rataye wuyarsa har sai ya mutu ko kuma ayi masa wata allura da ke kashe mutum cikin sauri.

A cewar alkalin, hujja da jawaban da faston ya yi sun nuna cewa ya aikata laifin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda Okoroafor ya kashe mawakiyar cocinsa

An tattaro cewa mawakiyar cocin, Orlunma Nwagba, ta ziyarci gidan faston da ke Oyigbo don tattaunawa kan zargin cikin da ya yi mata lokacin da ya yaudareta zuwa wani jeji sannan ya aikata ta'asar a wurare biyu mabanbanta.

Jami'an yan sandan jihar Ribas ne suka kama Fasto Okoroafor a ranar 17 ga watan Disambar 2017 bayan mijin Chigozie ya koka kan kisan mutanen uku a wurare daban-daban a karamar hukumar Oyigbo.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

Hawaye sun zuba yayin da Allah ya amshi ran kanin tsohon ministan shari'a Malami

A wani labari na daban, Allah ya yi wa Dr Khadi Zubairu Malami, kanin tsohon atoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, rasuwa.

Marigayi Zubairu ya rasu a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya a gidansa da ke Birnin Kebbi kuma tuni aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel