Sarkin Iwo Ya Shawarci 'Yan Najeriya Da Su Yi Hakuri Da Mulkin Shugaba Tinubu

Sarkin Iwo Ya Shawarci 'Yan Najeriya Da Su Yi Hakuri Da Mulkin Shugaba Tinubu

  • Babban basaraken masarautar Iwo a jihar Osun, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi ya shawarci ƴan Najeriya da su yi wa shugaba Tinubu uzuri
  • Babban basaraken ya ce cire tallafin man fetur da shugaba Tinuɓu ya yi, abu ne mai kyau wanda zai amfani ƴan Najeriya
  • Basaraken ya shawarci shugaba Tinubu da ya fara rabon kayan tallafi domin tsamo ƴan Najeriya daga ƙuncin da suka shiga saboda cire tallafin mai

Jihar Osun - Babban basaraken Iwo, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi, ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi haƙuri da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu wajen magance matsalolin tattalin arziƙin da ƙasar nan ke ciki. 

Oba Akanbi ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya sanar, ya zama wajibi domin rage asarar da ake tafkawa saboda masu kuɗi kawai tallafin ya ke ƙara azurtawa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Abubuwa 2 Da Ke Faruwa a Kasa Wadanda Tinubu Bai Yi Magana a Kansu Ba Ranar Da Aka Rantsar Da Shi

Sarkin Iwo ya shawarci 'yan Najeriya kan mulkin Tinubu
Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

Basaraken na jihar Osun ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakinsa, Alli Ibraheem, ya fitar a ranar Juma'a.

Ya bayyana shugaba Tinubu a matsayin masani kan mulki wanda ya damu da walwalar mutanen da ya ke mulki, inda ya ce cire tallafin man fetur ɗin zai amfani talakawan Najeriya nan gaba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban basaraken ya kuma buƙaci Tinubu da ya samar da hanyoyin da za su rage matsin lambar da tattalin arziƙin ƙasar nan ya ke fuskanta a dalilin cire tallafin man fetur ɗin, rahoton Punch ya tabbatar.

Oba Akanbi ya yi bayanin cewa tallafin man fetur wani shiri ne kawai na azurta wasu tsirarun attajiran Najeriya. Tallafin man fetur ɗin ba zsi taɓa bari ƙasar nan ta ci gaba ba.

Basaraken ya ce akwai alheri a cire tallafin man fetur

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC Kyari, Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Dole a Cire Tallafin Man Fetur

A cewar basaraken babu gwamnatin da zata iya kai labari idan tana biyan maƙudan kuɗaɗe a matsayin tallafin man fetur a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ɗin alheri ne ga ƴan Najeriya, inda ya buƙaci ƴan Najeriya da su kai zuciya nesa kan shugaba Tinubu.

Basaraken ya shawarci shugaban ƙasar da ya hanzarta fara rabon kayayyakin tallafi ga ƴan Najeriya domin rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ɗin ya jefa su a ciki.

Shekarau Ya Yi Hangen Nesa Ya Ba Tinubu Muhimmiyar Shawara

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi magana kan cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Tinubi ta yi.

Shekarau ya shawarci shugaba Tinubu da ya fara rabon kayan tallafi ga ƴan Najeriya domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ɗin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel