Shekarau Ya Yi Hangen Nesa Ya Ba Tinubu Muhimmiyar Shawara Kan Cire Tallafin Man Fetur

Shekarau Ya Yi Hangen Nesa Ya Ba Tinubu Muhimmiyar Shawara Kan Cire Tallafin Man Fetur

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ba gwamnatin shugaba Tinubu shawara kan cire tallafin man fetur
  • Shekarau ya bayyana cewa Tinubu ya yi kuskure wajen hanyar da ya bi ta sanar da cewa an cire tallafin man fetur ɗin
  • Sanatan ya ba gwamnatin Tinubu shawara da ta fara rabon kayayyakin tallafi domin rage raɗaɗin da cire tallafin man ya haifar

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa yakamata gwamnatin tarayya ta fara shirin gyaran ɓarnar da ta yi da tabbatar da cewa an raba tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ga ƴan Najeriya

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa, Shekarau ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, a cikin shirin gidan talbijin na Channels tv mai suna Politics Today.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: Reno Omokri Ya Lissafa Muhimman Sharudda 4 Da Ya Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Cika

Shekarau ya shawarci Tinubu kan cire tallafin mai
Malam Ibrahim Shekarau Hoto: Bbc.com
Asali: UGC

Shugaban ƙasa Bola Tinubu a lokacin da ya ke jawabi bayan an rantsar da shi, ya bayyana cewa lokacin biyan tallafin man fetur ya ƙare sannan ba a sanya shi a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023 ba.

Wannan furucin na Bola Tinubu ya sanya mutane sun yi rububin siyan man fetur inda samun man fetur ɗin ya zama jan aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shekarau ya bayyana cewa hanyar da Tinubu ya bi wajen sanar da cire tallafin ita ce ta sanya ƴan Najeriya suka shiga yin rububi wajen neman man fetur ɗin.

Shekaru ya bayyana cewa Tinubu ya sanar da cire tallafin ne cikin yanayi irin na mulkin soja.

Sanatan ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta bayyana ƙarara cewa za a cire tallafin man fetur, saboda babu shi a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Yabi Tinubu, Mutane Ana Kuka da Janye Tallafin Fetur

Shekarau ya shawarci Tinubu kan abinda ya dace ya yi

A kalamansa:

"Da ni na ke a matsayin Tinubu, da zan yi bayanin cewa tuni aka fara cire tallafin man fetur kuma ban adawa da hakan, za mu yi nazari akai mu ga haɗarin da ya ke tattare da yin hakan sannan mu tabbatar cewa mu na sane da abinda ya ke faruwa."
"A zancen gaskiya, ina tunanin yadda martanin da ƴan Najeriya suka yi ya kasance, ba abinda ba a yi zaton kasancewarsa ba ne."
"Yakamata kuma gwamnatin tarayya ta fito ta fara rabon kayayyakin tallafi sannan ta ba ƴan Najeriya dukkanin tabbacin da yakamata."

Reno Omokri Ya Shawarci Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

A wani labarin na daban kuma, Reno Omokri, tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan, ya yi magana kan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.

Reno ya lissafo wasu muhimman sharuɗɗa da yakamata gwamnatin Tinubu ta cika bayan ta zare tallafin man fetur ɗin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel