Shugaban NNPC Kyari, Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Dole a Cire Tallafin Man Fetur

Shugaban NNPC Kyari, Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Dole a Cire Tallafin Man Fetur

  • Babban manajan daraktan NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa Gwamantin Tarayya ba za ta iya ci-gaba da biyan kuɗaɗen tallafin man fetur ba
  • Ya ce yanzu haka NNPC na bin Gwamnatin Tarayya bashin kuɗaɗe da suka kai tiriliyon biyu da ɗigo takwas (N2.8t) kuma har yanzu gwamnatin ta gaza biya
  • Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin raba kayayyakin tallafi ga 'yan Najeriya domin rage tasirin wahalhalun da cire tallafin man fetur ɗin zai haifar

Babban manajan daraktan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya ce babu gudu babu ja da baya kan batun cire tallafin man fetur saboda Najeriya ba za ta iya ci-gaba da biyan tallafin ba.

Kyari ya zanta da manema labarai ne bayan ganawa da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ranar Alhamis, a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa dake Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Manajan NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Babu gudu ba ja da baya kan batun ta cire tallafin mai
Mele Kyari ya ce gwamnati ba za ta iya ci-gaba da biyan kuɗin tallafin man fetur ba. Hoto: The Cable
Asali: UGC

Matakin Tinubu na shan suka

Shugaba Bola Ahmed Tinubu jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya na 16, ya sanar da cire tallafin man fetur a hukumance.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai wannan matakin nasa na shan suka daga 'yan Najeriya saboda tsadar rayuwa da ta addabesu.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a ranar Laraba, ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ya haifar da ƙalubale sosai ga ‘yan Najeriya musamman ma waɗanda suke a jihohi.

Sai dai Mele Kyari ya ce kuɗaɗen tallafin da ake bin gwamnati sun yi yawa, yana mai jaddada cewa ƙasar har yanzu ta gaza biyan NNPC kuɗaɗen da take kashewa kan tallafin man fetur.

NNPC na bin Gwamnatin Tarayya bashi, In Ji Kyari

Sai dai kuma ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bayar da tallafi ga al'umma domin daƙile tasirin wannan mataki da gwamnati ta ɗauka.

Kara karanta wannan

Shekarau Ya Yo Hangen Nesa Ya Ba Tinubu Muhimmiyar Shawara Kan Cire Tallafin Man Fetur

Kyari ya ce a shekarar 2022, gwamnati ta biya kuɗaɗen na tallafi, amma a shekarar 2023, ko sisi ba a bayar ba da sunan tallafi.

A rahoton Guardian, Kyari ya ƙara da cewa yanzu haka suna bin gwamnati bashin kuɗaɗen tallafi da suka kai tiriliyon biyu da ɗigo takwas (N2.8t).

Dan majalisa ya koma hawa keke saboda da tsadar fetur

A wani labarin mai alaƙa da janye tallafin mai, kun ji labarin wani ɗan majalisan jihar Adamawa da ya ajiye motarsa ya koma hawa keke saboda tsadar man fetur.

Ɗan majalisar yace wannan nau'ine na zanga-zangar nuna ƙin amincewa da cire tallafin man da gwamnatin tarayya ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel