‘Yan Bindiga Sun Yi Alkawarin Cigaba da Kashe-Kashe Cikin Watan Azumi a Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Yi Alkawarin Cigaba da Kashe-Kashe Cikin Watan Azumi a Zamfara

  • Mutanen da ke rayuwa a karkarorin da ke karkashin karamar hukumar Birnin Magaji sun shiga uku
  • ‘Yan bindiga sun hana kauyuka sakat, su na so a cire sojojin da suke gadin Bayin Allah daga ta’adinsu
  • Mazauna wadannan garuruwan sun bayyana irin kisan dauki dai-daya da ake yi masu kwanan nan

Zamfara - A garin Birnin Magaji da ke jihar Zamfara, ‘yan ta’adda sun sha alwashin cigaba da kai wa mutane hari har sai an janye sojojin da aka zuba.

Wasu mazauna Birnin Magaji sun shaidawa Premium Times cewa miyagun ‘yan bindigan da suka addabe su, sun ce dole sai sojoji sun bar yankin na su.

An dade ana fama da kashe-kashe, satar dabbobi da garkuwa da mutane a Zamfara.

Jaridar ta tatatuna da wasu daga cikin mazauna kauyukan Mazauda, Nasarawa Mai layi da Gidan Kane inda aka hallaka mutane 16 a ‘yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Rasa Rayuka Yayin da Wani Gini Ya Tumurmushe Mutane a Abuja Cikin Azumi

An kashe mutane a kauyuka 3

Wani Bawan Allah da gidansa yake kauyen Gidan Kane, ya ce ‘yan bindiga sun kai munanan hari a garuruwa uku a daren Litinin dinnan da ta gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sun kashe mutane biyu a Tunkuda, biyu a Mashayawo da mutum hudu a Mazauda. Sun rika bin kauye zuwa kaye su na addabar mutane.
A ranar Litinin, sun kai hari a kauyen Maituri, sun hallaka wasu mutane uku, kauyukan nan duk su na karkashin mazabar Gusami Hayi ne.
‘Yan Bindiga
Wasu 'Yan sa kai a Zamfara Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Majiyar ta ce a yammacin Lahadi ne aka shiga Tungar Danjuma da Kiri Fada, aka kai wa Bayin Allah hari a lokacin da suke kammala sallah a masallaci.

'Yan bindiga sun bada sharadi guda

A Mazauda, wani mutumi ya ce ‘yan ta’addan sun fada masu sai an janye sojoji za sus amu sauki. Yawan sojojin da ke yankin ya inganta tsaro a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Assha: Mafarauta sun yiwa mutum kallon zomo, sun dirke shi da bindiga har barzahu

An jibge sojojin ne a kauyen Kara Zube, amma mutanen garuruwan sun ce da an kira jami’an tsaro, suke kawo dauki idan ‘yan bindiga na shirin kai masu hari.

Blueprint ta ce wasu da ke zama a Gidan Kane sun ce sojojin sun matsawa ‘yan ta’addan lamba, don haka su ce dole su bar yankin, ko su rika auka masu.

Mohammed Shehu wanda shi ne Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara, bai amsa wayar salularsa ba da aka tuntube shi domin jin halin da ake ciki.

Zaben Gwamnan Adamawa

Rahotanni sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya bukaci ‘Yan Sanda su yi bincike a kan zaben Adamawa, inda wani jami’in REC ya jefa mutane a rudani.

Lura da abin da ya faru a karashen zaben na Adamawa, Tinubu ya yi kira da a shirya cikakken bincike, sannan wadanda suka sha kashi su bi dokar kasa.

Kara karanta wannan

A Gab da Sallah, Yan Bindiga Sun Halaka Magajin Gari, Sun Aikata Mummunar Ta'asa a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel