Matar Aure Ta Garzaya Kotu Neman a Datse Igiyar Aurenta Da Mijinta

Matar Aure Ta Garzaya Kotu Neman a Datse Igiyar Aurenta Da Mijinta

  • Wata matar aure mai suna Ganiyat Yaya tana neman mijinta Tajudeen Yaya da ya sawwaƙe mata bayan ya tafi ya barta da ƴaƴa mata huɗu
  • Ta zarge mijin na ta da yin watsi da kulawa da su, nuna tsangwama kan ƴaƴansu da rashin kyautata mata a zaman aurensu
  • Tajudeen ya musanta dukkanin zarge-zargen da ta ke masa inda ya bayyana cewa a shirye ya ke su ci gaba da zama tare

Jihar Oyo - Wata matar aure ta shigar da ƙara tana neman mijinta ya sake ta, bayan ya tafi ya bar su ita da ƴaƴanta guda huɗu har na tsawon wata shida.

Ganiyat ta gayawa kotun kostamare ta Mapo a birnin Ibadan na jihar Oyo, cewa ba ta son ci gaba da zaman aure da Tajudeen Yaya, wanda ta zarga da rashin sauke nauyin da ke kansa.

Matar aure na neman kotu ta raba aurenta da mijinta
Matar auren tace ta gaji Hoto: Shuttlestock
Asali: Getty Images

Ya daina sauke nauyin da ya rataya a kansa

A cewar Ganiyat, mijinta ya daina kula da su sannan ya ƙi samar musu da abinci, karatu da kuɗin asibiti. Ta kuma yi iƙirarin cewa yana nuna tsangwama kan ƴaƴansu saboda dukkanin su mata ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ganiyat ta bayyana cewa mijinta bai kyautata mata sannan a wasu lokutan har tsine mata ya ke yi yana hanata shiga gidan.

Ta ƙara da cewa har iyaka ya yi mata da ita da ƴaƴanta kan kada su riƙa amfani da wasu sassa na gidan da suke zaune.

Tana neman kotu ta bar yaran a hannunta

Ta roƙi kotun da ta raba aurensu sannan ta bata ikon riƙe yaran a hannunta. Ta kuma nemi kotun da ta sanya shi ya riƙa kula da su musamman ɓangaren karatu da lafiya.

Tajudeen ya musanta dukkanin zarge-zargen da ta ke yi masa, inda ya bayyana cewa bai tafi ya bar iyalansa ba sannan yana son ƴaƴansa ba tare da la'akari da jinsin su ba.

Ya kuma ƙara da cewa bai hana matarsa shigowa gidan ba ko yi mata iyaka da wani ɓangare. Ya zarge ta da zama kasalalliyar mace mara ganin mutuncinsa.

Ya bayyana cewa a shirye ya ke su ci gaba da rayuwar aure idan matarsa za ta sauya halayenta ta ba shi haɗin kai, cewar rahoton Tribune.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 20 ga watan Yuli, sannan ta shawarci ma'auratan da su yi ƙoƙarin sulhunta tsakaninsu.

Matar Aure Za Ta Dawo da Sadakin N80k a Gaban Kotu Don a Tsinke Igiyar Aurenta

Wata matar aure ta shirya dawo da sadakin N80k, domin a datse igiyar auren da ke tsakaninta da mijinta.

Wani alƙalin kotun shari'ar musulunci ne a jihar Kaduna, ya bayar da umarnin ga matar auren bayan ta bayyana cewa ta gaji da zaman aure tare da mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel