Babu Kari: Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Bayyana Adadin Abin da Ya Mallaka Bayan Sauka Daga Mulki

Babu Kari: Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Bayyana Adadin Abin da Ya Mallaka Bayan Sauka Daga Mulki

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika takardun da ke bayyana adadin dukiyar da ya mallaka ga hukumar da’ar ma’aikata ta CCB
  • Garba Shehu, tsohon kakakin Buhari ne ya bayyana hakan, inda yace Buhari bai samu kari kan wasu daga cikin kadarorinsa ba
  • Haka nan, ya ce Buhari bai bude sabbin asusun banki ba, kuma ba a binsa bashin ko anini, amma dabbobinsa sun ragu saboda yawan kyauta

Daura, jihar Katsina – Kamar yadda doka ta tanada, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana adadin dukiya da kadarorin da ya mallaka ga hukumar da’ar ma’aikata ta CCB.

Wannan na zuwa ne ta bakin tsohon kakakin Buhari, Garba Shehu a ranar Asabar 3 ga watan Yuni 23 lokacin da ya yada sanarwar hakan a kafar Twitter.

Shehu, a sanarwar da ta yada wacce Legit.ng Hausa ta gani ya nuna rasitin tabbatar da cewa Buharin ya ayyana adadin dukiyarsa.

Buhari ya fadi yawan dukiyarsa bayan kammala mulki
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: @GarbaShehu
Asali: UGC

Kadarorin Buhari masu motsi ba su karu ba

A cewar Shehu, kirge ya nuna cewa kadarorin da tsohon shugaban kasar ke da masu motsi, irinsu dabbobi basu karu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, Buhari a nan gida Najeriya ko a waje kuma bai kara bude sabbin asusu na banki ba baya ga wanda yake dashi guda daya na bankin Union mai ofishi a Kaduna.

A cewarsa:

“Bai karbi wani bashi ba kuma ba shi da wani abu a kansa.
“Adadin dabbobin da ke gonarsa sun ragu kadan saboda adadin da ya bayar a matsayin kyauta a cikin shekaru hudu da suka gabata."

A dokance a Najeriya, kowane shugaban da ya rike kujerar siyasa dole ne ya bayyana adadin dukiyar da ya mallaka kafin hawa mulki da kuma bayan kammala yiwa kasa hidima.

Tinubu ya karbi mulkin Najeriya daga hannun Buhari, ya cire tallafin man fetur

A wani labarin, kunji yadda aka rantsar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin sabon shugaban kasa a Najeriya da kuma matakan da ya fara dauka nan take.

Rahoto ya bayyana cewa, Tinubu ya janye tallafin man fetur nan take da ya karbi mulkin Najeriya daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce, inda ‘yan kasa da yawa ke ganin za a samu tsaiko a mulkin sabon shugaban na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel