"Tallafin Mai Ya Tafi" Shugaba Tinubu Ya Fara Daukar Matakai Masu Tsauri

"Tallafin Mai Ya Tafi" Shugaba Tinubu Ya Fara Daukar Matakai Masu Tsauri

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce zancen tallafin man fetur ya kare a Najeriya, gwamnatinsa ba zata iya ba
  • Tinubu ya sha alwashin karkatar da kuɗin tallafin zuwa bangaren ilimi, noma da kiyo, kiyon lafiya da sauran ayyukan raya ƙasa
  • Wannan kalaman na kunshe a cikin jawabinsa a wurin bikin mika mulki bayan karewar wa'adin tsohon shugaban kasa, Buhari

Abuja - Shugaban kasan Najeriya da ya hau kan madafun iko yau, Bola Ahmed Tinubu, ya ce tallafin man fetur ya zo karshe a karkashin sabuwar gwamnatinsa.

A rahoton The Nation, Sabon shugaban ƙasan ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa na wurin rantsarwa da ya gudana a filin Eagle Square ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.

Bola Tinubu.
"Tallafin Mai Ya Tafi" Shugaba Tinubu Ya Fara Daukar Matakai Masu Tsauri Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya yi bayanin cewa bisa la'akari da tsarin da ke ƙunshe a kasafin kuɗin 2023, gwamnatin tarayya zata daina biyan tallafin kuɗin Fetur daga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Fetur Ya Haura N300 a Gidajen Mai Daga Jin Bola Tinubu Ya Sanar da Janye Tallafi

A ruwayar Daily Trust, Tinubu ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun yaba da matakin da gwamnati mai barin gado ta ɗauka na rabuwa da tallafin man fetur, wanda kowa ya sani yana kara wa mai karfi karfi ne kawai."
"A halin yanzu hankali ba zai ɗauki adadin makudan kudin da suke ƙaruwa ba da sunan Tallafi, maimakon haka zamu sauya akalar kuɗin zuwa fannin ayyukan raya ƙasa, Ilimi da lafiya da ayyuka."
"Idan aka maida akalar waɗan nan kudaɗen a fannonin nan zai kara inganta yanayin rayuwar miliyoyin 'yan Najeriya."

Bugu da ƙari, Sabon shugaban ƙasa yace zai duba korafe-korafen da suka isa kan teburinsa kan yawaitar kuɗin haraji da nufin bunkasa tattalin arziki da jawo hankalin masu zuba hannun jari.

Bayan lashe zaben shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya mika ragamar jagoranci ga Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rudani Yayin Da Rahoto Ya Yi Ikirarin Tinubu Ya Yi Nade-Naden Farko Bayan Rantsarwa

Sarki Aminu Ado Bayero Ya Aika Bukata a Wajen Tinubu Kafin Ya Shiga Aso Rock

A wani rahoton kuma Sarki Aminu Ado Bayero Ya Aika Bukata a Wajen Tinubu Kafin Ya Shiga Aso Rock.

Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira ga Asiwaju Bola Tinubu a matsayinsa na zababbe kuma shugaba mai jiran gado.

Vanguard ta kawo rahoto a yammacin Juma’a cewa Alhaji Aminu Ado Bayero ya na so a kafa ma’aikata da za ta rika kula da harkokin addini a kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel