Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hadu da Hafsoshin tsaro, sun yi kusan awanni uku su na tattaunawa
  • A zaman da aka yi a fadar Aso Rock Villa, Shugabannin sojoji da tsaro sun yi bayanin halin da ake ciki
  • Tinubu ya nuna ba zai ba ‘yan ta’adda damar cin karensu babu babbaka ba, ya kuma bukaci ayi aiki tare

Abuja - Sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da hafsoshin tsaro kuma ya ja-kunnensu a game da cin dunduniyar juna a wajen aiki.

Abin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya bukata daga shugabannin tsaron shi ne su yi aiki tare cikin hadin-kai da juna, Daily Trust ta fitar da rahoton.

Shugaban kasar ya bukaci hafsoshin sojoji da takwarorinsu su hada-kai domin a yaki ‘yan bindiga, ta’addanci, tada kafar baya, satar mai da fashin kan ruwa.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: NNPC Ya Fadi Sabon Shirin Bola Tinubu Tun da Farashi Ya Kai N550

Tinubu
Shugaba Tinubu tare da Hafsoshin Tsaro, shugabannin NIA, NSA da IGP Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Monguno ya yi karin haske

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya shaidawa manema labarai wannan a Aso Rock.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babagana Monguno ya yi magana da manema labaran bayan zaman farko da suka yi da sabon shugaban kasar wanda su ka shafe sama da awanni biyu.

An rahoto Monguno ya na cewa Shugaba Bola Tinubu ya bukaci a rika tuntubar juna a kai-kai.

Baya ga haka, Mai girma shugaban na Najeriya ya nemi a rika daukar mataki a lokacin da ya dace idan an samu rahoto na tsaro ko an yi zaman kwamiti.

Masu fasa bututun mai

A jawabin da NSA din ya yi, ya nuna cewa sabon shugaban kasar ba zai yarda a rika satar danyen man kasar ba, don haka ya bukaci hafsoshin su tashi tsaye.

Kara karanta wannan

Shugaban Ma'aikatan Tinubu: A Karshe Femi Gbajabiamila Ya Yi Martani, Ya Fadi Yadda Abun Yake

Haka zalika Tinubu wanda ya shiga ofis a ranar Litinin ya shaida cewa gwamnatinsa za ta kawo gyare-gyare ga sha’anin tsaro, a canza tsarin da ake tafiya a kai.

A taron, shugaba Tinubu ya dauki lokaci wajen yabawa jami’an tsaro kan kokarin da suke yi, har ya yi ta’aziyyar wadanda aka rasa a wajen yi wa kasa hidima.

Rahoton ya ce a wajen ne hafsoshin tsaro su ka fahimci inda Tinubu ya dosa da manufarsa kan batun tsaro, bayan ya saurari jawabi daga kowane bangare.

"Zai shiga kawo garambawul da-dama ga tsarin tsaro, zai duba rashin nasarar da aka yi a bangaren ruwa, musamman ba zai yarda da sha’anin satar mai ba."

- Babagana Monguno

Gwamnatin Ribas ta fara aiki

Rahoto ya zo cewa sabon Gwamna Siminalayi Fubara ya dawo da wasu Kwamishinoni da su ka yi aiki da Gwamna Nyesom Wike da ya sauka.

An rantsar da Zacheous Adango, Alabo George Kelly, Chinedu Mmom da Isaac Kamalu da George Nweke a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel