Bukatun Farko: NANS Ta Lissafo Abubawan da Ta Ke Bukata Gwamnatin Tinubu Ta Aiwatar

Bukatun Farko: NANS Ta Lissafo Abubawan da Ta Ke Bukata Gwamnatin Tinubu Ta Aiwatar

  • Wani mai magana da yawun Kungiyar Daliban Najeriya (NANS), Awoyinfa Opeoluwa ya bayyana bukatunsu a sabuwar gwamnati
  • Dalibin ya kirayi Shugaba Bola Tinubu da ya bai wa ilimi muhimmanci a gwamnatinsa don samar da ci gaba mai dorewa
  • NANS har ila yau, ta bukaci Tinubu da ya yi aiki tukuru don nemo hanyoyin da za a magance matsalolin tsaro a kasar

Jihar Osun – Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) reshen Kudu maso Yamma ta lissafo abubuwan da ta ke bukatan Shugaba Tinubu yafi bai wa muhimmanci.

Da yake magana da Legit.ng a ranar Alhamis 1 ga watan Mayu, mai magana da yawun kungiyar, Awoyinfa Opeoluwa ya ce gwamnatin Tinubu za ta baiwa harkan ilimi muhimmanci.

Kungiyar NANS
NANS Ta Lissafo Abubawan da Ta Ke Bukata Gwamnatin Tinubu Ta Aiwatar. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Awoyinfa Opeoluwa.
Asali: Facebook

A rahoton da aka fitar a shekarar 2022, akalla mutane miliyan 90 ne ba su da aikin yi a Najeriya mafi yawansu suna da shaidar kammala digiri.

Ya ce gwamnatin dole ta samar da ayyukan yi

A hirar tasa da Legit.ng, Awoyinfa ya bayyana cewa dole gwamnati ta samar da ayyukan yi musamman ga matasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“A matsayin mu na dalibai, muna burin cewa gwamnatin nan za ta yi abin kirki, muna sa ran za ta bai wa harkan ilimi kulawa da samar da ayyukan yi ga matasa.”

Ya roki Tinubu da ya kare dalibai lokacin da suke makaranta

Ya kirayi gwamnatin da ta kawo ayyukan raya kasa da samar da aikin yi, ya kuma roki Tinubu da ya kula da kare dalibai da kuma malamansu a lokacin da suke makaranta.

Ya kara da cewa:

“Muna tsammanin gwamnati za ta inganta harkokin jin dadi da samar da yanayi mai kyau don inganta kasuwanci wanda zai samar da ayyukan yi ga wadanda suka gama makaranta.

“Dadi da kari akwai bukatar gwamnati ta samar da tsaro da tabbatar da tsaron ‘yan kasa musamman dalibai.”

Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago Akan Cire Tallafi

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta NLC da kuma ta 'Yan Kasuwa, TUC sun gana da gwamnatin Tarayya don shawo kan matsalar farashin mai bayan cire tallafi.

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai a ranar Litinin 29 ga watan Mayu yayin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel