Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

  • Babu abin da ke nuna tsohon Kwamishinan Legas ya zama mai magana da yawun Bola Tinubu
  • Da aka yi magana da shi, Dele Alake ya ce ba a kai ga ba shi mukami a sabuwar gwamnati ba
  • Haka zalika ana yada jita-jitar Olusegun Dada ya zama Hadimin sabon shugaban na Najeriya

Abuja - Tsohon Kwamishinan yada labarai da dabarun jihar Legas, Dele Alake ya musanya rade-radin cewa an ba shi mukami a sabuwar gwamnati.

Rahotanni na yawo cewa Dele Alake ya zama mai magana da yawun bakin Bola Ahmed Tinubu, amma ya shaidawa The Cable cewa ba haka ba ne.

Da ya zanta da jaridar, tsohon Darektan sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban na APC ya ce jerin mukaman da aka fitar duk na bogi ne.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Sabon Shugaban Kasa
Bola Tinubu da mai dakinsa Hoto: @opeadelani
Asali: Twitter
“Labarin bogi ne. Ina yawon mamaki idan ‘yan jarida su ka gagara gane labaran bogi wadanda ba su da tushe.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Dele Alake

Wanene Dele Alake?

Alake kwararren ‘dan jarida ne wanda ya yi aiki da National Concord ya rika yi mata rubuce-rubuce, har ta kai ya zama babban editanta a 1995.

Bayan shekara da shekaru ya na aikin jarida, sai Tinubu ya ba shi Kwamishinan labarai a gwamnatinsa tun daga 1999 har zuwa Mayun 2007.

A lokacin da Muhammadu Buhari zai yi takara a 2015, Alake ne ya zama Darektan yada labarai da sadarwa, karon farko kenan da ya dawo siyasa.

Haka a zaben 2023, ‘dan jaridar ya yi aiki da kwamitin yakin neman zaben APC.

Rahoton ya ce Femi Fani Kayode ne ya fara yada wannan labarin karya a shafinsa, ba wannan ne karon farko da tsohon Ministan ya yi irin haka ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Nade-Naden Mukamai 7 Ana Tsakiyar Rantsar da Tinubu

Olusegun Dada ya zama S.A?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har zuwa safiyar Laraba babu abin da ke tabbatar da cewa Olusegun Dada ya zama Hadimin sabon shugaban kasa.

A shafinsa na Twitter na @DOlusegun ya nuna shi ‘dan jam’iyyar APC, amma babu inda ya nuna karara ya na taimakawa Tinubu a kafofin zamani.

Sai dai tsohon ‘dan takaran kujerar shugaban matasan APC na kasa ya na yada hotunan Tinubu, babu mamakin nan gaba a ba shi mukamin.

Shari'ar zaben 2023

A yau ne aka ji labari Lauyan PDP, Eyitayo Jegede SAN ya kawo sakamakon zaben shugaban kasa na jihohi 36 da Abuja a gaban kotun karar zabe.

Shi ma ‘Dan takaran LP, Peter Obi ya fara kawo shaidu domin ya nuna an taba kama Bola Tinubu cikin harkar kwayoyi a shekarun baya a Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel