An Tura Maniyyata Zuwa Aikin Hajji a Saudi Su Kadai Saboda Rashin Biyan Kudi

An Tura Maniyyata Zuwa Aikin Hajji a Saudi Su Kadai Saboda Rashin Biyan Kudi

  • Babu ma’aikacin hukumar alhazai da zai yi wa maniyyatan jihar Filato rakiya zuwa Saudi Arabiya
  • Idan aka tafi a haka, maniyyatan kadai za a bari a kasa mai tsarki, babu wasu masu yi masu jagora
  • Ana zargin cewa ba a aikawa hukumar alhazai kudi a kan lokaci ba ne har aka canza Gwamnati

Plateau - Musulman da ke shirin yin aikin hajjin wannan shekara daga jihar Filato, su na tsoron cewa za a samu matsala a ibadarsu a dalilin sha’anin kudi.

Premium Times ta kawo rahoto cewa akwai yiwuwar wannan karo 'yan tawagar hukuma ba za su bi jiragen Filato ba domin ba a kai kudin hajjin jihar ba.

Maniyattan su na tsoron cewa ma’aikatan lafiya da malamai da suka saba bin mahajjata domin yi masu jagora duk shekara, ba za su bi tawagar bana ba.

Aikin Hajji
Wasu mahajjatan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton ya na zargin cewa tsohuwar gwamnatin da ta shude ba ta kai kudin hajjin mutanen jihar Filato kafin ta mika mulki ga sabuwar gwamnatin nan ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai jan aiki!

Idan har aka tafi aikin hajji ba tare da ma’aikatan hukumar alhazai da malaman lafiya ba, za a iya fama da matsalolin wurin kwana, abinci da kiwon lafiya.

Akwai bukatar ma’aikatan hukumar alhazai su raka masu niyyar sauke farali. Jami’an kowace jiha suke yi masu hidima tare da sama masu malamai.

Jaridar ta ce wadannan ma’aikata ne su ke taimakawa a kowace rana wajen rabon abinci, kuma su na saukaka mahajjata wajen zirga-zirga a kasa mai tsarki.

Kadai ma aka fara gani?

Wani Bawan Allah da jirginsu ya tashi a ranar Juma’a, ya ce an bar su a wani irin yanayi, lamarin zai iya cabewa yayin da ake shirin tafiya zuwa Madaina.

Tun a jirgin sama, wannan maniyyaci ya ce sun samu matsalar farfadiya, amma babu malamin kiwon lafiya da zai iya taimakawa mai fama da larurar.

Sai daga baya su ka gano babu ma’aikacin da ke tare da su, masu aikin hajji ne kurum a tafiyar.

An nemi jin ta bakin Sakataren hukumar Alhazai ta kasa, Malam Auwal Abdullahi domin jin gaskiyar batun, amma ba a same shi ta waya ko sakon salula ba.

Tashin jirgin Nigeria Air

Kafin ya bar ofis, an ji labari Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika ya dage cewa jirgin Nigeria Air Limited zai fara aiki kafin karshen wa’adin gwamnatinsu.

Sirika ya yi ikirarin sun tanadi abin da ake bukata, amma sai daf da Muhammadu Buhari zai bar ofis aka ga jirgi daya, kuma har yau babu duriyarsa a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel