Dadiyata: Sabon Gwamnan Kano Ya Yi Alkawarin Binciken Masoyinsu Da Aka Sace a 2019

Dadiyata: Sabon Gwamnan Kano Ya Yi Alkawarin Binciken Masoyinsu Da Aka Sace a 2019

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi alkawari ba za ta bari maganar dauke Dadiyata ta tafi a banza kawai ba
  • Sabon Gwamnan jihar Kano ya ce za su hada-kai da jami’an tsaro domin a gano wannan Bawan Allah
  • Abba Gida-Gida ya tuno da babban masoyin na Kwankwasiyya yayin da aka rantsar da shi a kan mulki

Kano - Sabon Gwamnan jihar Kano ya shiga ofis a ranar 29 ga watan Mayun 2023, kuma tuni ya nuna ba da wasa ya zo mulki ba.

Abba Kabir Yusuf wanda ya fi shahara da Abba Gida-Gida, ya yi alkawarin yin bincike kan bacewar Abubakar Idris (Dadiyata).

A jawabin da ya yi bayan ya karbi ragamar mulkin jihar Kano, Abba Gida-Gida ya dauko maganar Dadiyata wanda aka sace tun 2019.

Dadiyata
Abubakar Dadiyata da Abba Gida Gida Hoto: Dadiyata / EngrAbbaKYusif
Asali: Facebook

Abba Kabir Yusuf wanda ya fi shahara da Dadiyata, ya yi alkawarin yin bincike a game da bacewar Malam Abubakar Idris (Dadiyata).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a Twitter, sabon Gwamnan ya jaddada jawabinsa a filin wasan Sani Abacha.

Gwamnan ya ce har yau ba su manta da wannan Bawan Allah wanda masoyi ne kuma ‘dan tafiyar Kwankwasiyya wanda ya bace ba.

Na yi magana a jawabina

"Kafin yanzu, a jawabin bayan karbar rantsuwana, Na shaida cewa ba za mu manta da ‘dan tafiyarmu kuma masoyi mai daraja…
…Abubakar Dadiyata wanda wasu mutane da ba a san su ba, su ka dauke shi ido yana ganin ido fiye da shekaru uku da suka wuce.
Gwamnatin jihar Kano za ta dauko batunsa tare da duk wasu jami’an tsaro na kasar nan da abin ya shafa domin a kubutar da shi…

Sannan a hukunta masu hannu a lamarin."

- Abba Kabir Yusuf

Wanene Dadiyata?

Legit.ng Hausa ta na da masaniya cewa Abubakar Idris wani matashin malamin jami’a ne wanda ya yi suna sosai a tafiyar Kwankwasiyya.

Baya ga goyon bayan Rabiu Kwankwaso, Dadiyata kamar yadda aka fi saninsa a kafofin sada zumunta, ya kan caccaki gwamnatin APC.

A ranar 1 ga watan Agustan 2019, aka wayi gari da lamarin cewa wasu ‘yan bindiga sun je har gida sun sauke Dadiyata, har yau babu labarinsa.

Bichi ya zama SSG

Jim kadan bayan rantsar da shi, an ji labari Abba Gida Gida ya fara aiki a kan kujerar Gwamna, ya nada sakataren gwamnati da wasu mukamai.

Babban malamin nan, Dr. Sani Ashir ya shiga hukumar kula da jin dadin alhazai bayan sabuwar gwamnati ta kori shugabannin hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel