El-Rufai Ya Gayyaci Kwankwaso Kaddamar da Ayyukan Karshe Da Ya Yi a Kaduna

El-Rufai Ya Gayyaci Kwankwaso Kaddamar da Ayyukan Karshe Da Ya Yi a Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna ya gayyaci Rabi’u Musa Kwankwaso domin kaddamar da wasu ayyuka
  • Tsohon Gwamnan na Kano zai bude tituna da sabuwar kasuwar da Nasir El-Rufai ya gina a Kaduna
  • Watakila wadannan za su zama ayyukan karshe da Gwamna mai barin-gado ya yi a jihar Kaduna

Kaduna - A yau Juma’a, 26 ga watan Mayu 2023, ana sa rai Rabi’u Musa Kwankwaso zai ziyarci jihar Kaduna domin bude wasu ayyuka.

Legit.ng Hausa ta samu rahoto daga majiya dabam-dabam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai kaddamar da ayyukan Nasir El-Rufai.

Da yake magana a shafinsa na Facebook, wani hadimin ‘dan siyasar mai suna Ibrahim Adam ya tabbatar da labarin da yake ta yawo.

Kwankwaso a Minna
Rabiu Musa Kwankwaso a Minna Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Malam Ibrahim Adam ya nuna mai gidansa zai bude kasuwa da kuma wasu hanyoyi da gwamnatin Nasir El-Rufai ta gina a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Iyalin Tsohon Gwamna Sun Ba El-Rufai Hakuri a Kan Karbe Masu Filaye 9 a Kaduna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan Allah ya so, gobe (yau) Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso zai hadu da Gwamna Nasir El-Rufa’I na jihar Kaduna domin kaddamar da titin School road, titin Emir road da sabuwar kasuwar zamani ta Unguwar Rimi da ke garin Kaduna."

- Jawabin Hadimin Rabiu Kwankwaso

Hakan ya na zuwa ne jim kadan bayan Kwankwaso ya gabatar da lacca ta musamman wajen shirin rantsar da sabon Gwamnan jihar Neja.

‘Dan takaran shugaban kasar ya jagoranci laccar da aka shirya ranar Alhamis a Minna.

Kwankwaso ya iso Kaduna

Legit.ng Hausa ta fahimci tawagar tsohon Gwamnan na Kano ta iso garin Kaduna da yammacin jiya bayan gama taron da aka yi a Neja.

"Mun gode Mallam @elrufai. Allah ya taimake ka. Dukkanmu mu na godiya."

- Fatima Gambo Raka

"Abba wai dama mallam da madugu ana tare?"

Kara karanta wannan

Zaman da Kwankwaso Ya Yi da Tinubu a Faransa Zai Iya Canza Siyasar APC da Majalisa

- Awaisu Kabir

Mahmoud DakinGari,Esq yake cewa da alama garin Kaduna zai zama ja-wur a yau saboda ziyarar jagoran darikar siyasar Kwankwasiyya.

Tambayar da El Tama007 yake yi shi ne meya hana a gayyaci irinsu Gwmana Abdullahi Ganduje?

Kabeer Muhd mai suna @kabeerfawzan a Twitter, cewa kurum ya yi Madugu!

Yusuf Jamilu Baita ya na ganin hakan ya nuna Rabiu Kwankwaso jagora ne a Arewacin Najeriya.

Gobara a gidan Ganduje

A baya an samu labari gobara ta tashi a gidan da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje ya koma, hakan ya jawo aka yi asarar dukiya.

Kakakin Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da wannan. A daren Litinin wutar ta tashi a gidan a Nasarawa GRA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel