Iyalin Tsohon Gwamna Sun Ba El-Rufai Hakuri a Kan Karbe Masu Filaye 9 a Kaduna

Iyalin Tsohon Gwamna Sun Ba El-Rufai Hakuri a Kan Karbe Masu Filaye 9 a Kaduna

  • Nasir El-Rufai ya karbe wasu filaye da ake tunanin tsohon Gwamnan jihar Kaduna ya mallaka
  • Kamfanin tsohon Gwamnan ya rubutawa Gwamnati wasika, ya bada uzurin abin da ya hana gina filayen
  • Wasikun sun nuna ba haka kurum aka dauki tsawon lokaci ba tare da an gina wadannan fuloti ba

Kaduna - Kamfanin Canes Properties Limited ya rubuta wasika zuwa ga Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a dalilin karbe masa filaye.

Rahoto ya fito daga Premium Times cewa kamfanin ya roki Malam Nasir El-Rufai ya kara masa lokaci domin ya iya gina filayen da gwamnatinsa ta karbe.

Dangin Ahmed Muhammad Makarfi wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007 ke da iko da kamfanin, Ibrahim Mohammed Makarfi ne babban manajansa.

El-Rufai
Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @ GovKaduna
Asali: Twitter

Wasiku hudu da kamfanin na Canes Properties Limited ya aikawa Gwamna sun bada uzuri kan abin da ya hana a gine filayen tsawon shekarun da aka dauka.

Kara karanta wannan

NNPC Ta Ci Gaba Da Aikin Tono Mai a Borno Bayan Shekaru 6 Da Dakatarwa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da wasikun su ka kunsa

A game da fuloti da aka karbe mai lamba KDL 53874 a unguwar Mogadishu, kamfanin ya ce su na neman shekara guda domin gina rukunin shaguna.

Wasikar ta nuna an gabatar da takardar zanen ginin da za ayi, ana jiran amincewar KASUPDA.

Wasika ta biyu ta nuna Makarfi zai bukaci karin watanni uku domin yin karin gine-gine a filayensa masu lamba: KDL 01868, KDL 79707 da kuma KDL 79709.

Rahoton yace a game da sauran fulotin filin mai lamba KDL 264596, kamfanin tsohon Gwamnan ya na jiran takardun CofO daga hannun Gwamnatin Kaduna.

Canes Properties Ltd ya ce ya biya duk kudin da ake bukata, kuma ya kai takardu gaban KASUPDA.

Uzurin da kamfanin ya bada na rashin gina fili mai lamba KDL 40546 shi ne hanyar ruwa ta bi ta kan fulotin, wannan ne bayanin da aka yi a wasika ta hudu.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Jaridar ta tuntubi Ibrahim Makarfi domin jin ta-cewarsa, amma bai amsa waya ba. Shi ma Hadimin Gwamnan Kaduna, Muyiwa Adekeye bai dauki waya ba.

A ranar 29 ga watan Mayun nan ne wa’adin Malam Nasir El-Rufai zai cika, zai sauka daga mulki.

An nada Kwamishinoni a RMFAC

A yau ne aka ji labari Majalisar FEC tayi zaman da zai kasance na karshe a tarihin gwamnatin Muhammadu Buhari, a mako mai zuwa za a canza gwamnati.

A taron da aka yi, Shugaban kasa ya rantsar da Kwamishinonin hukumar RMFAC. A cikinsu akwai Rekiya Ayuba-Haruna da Hauwa Aliyu da Sanata Ayogu Eze.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng