Kwankwaso da Jerin Yan Siyasa Daga Jam’iyyun Adawa 5 da Ka Iya Samun Kujeru Masu Tsoka a Mulkin Tinubu

Kwankwaso da Jerin Yan Siyasa Daga Jam’iyyun Adawa 5 da Ka Iya Samun Kujeru Masu Tsoka a Mulkin Tinubu

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu bayan kammala wa’adin shugaba Muhammadu Buhari da ya fara mulki a 2015.

Gabannin rantsar da shi, zababben shugaban kasa Tinubu ya kulla alaka da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da suka hada da ‘yan jam’iyyun adawa.

Bayan sanar da shi a matsayin zababben shugaban kasa a zaben da aka gudanar a watan Faburairu, Tinubu a ya sha kiran a yi hadaka don kafa gwamnatin gamayya da za ta kawo ci gaba ga kasa.

Jerin wadanda ka iya tashi da kujera a mulkin Tinubu
Tinubu da wasu manyan siyasan Najeriya | Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike
Asali: Twitter

A kasa, jerin sunayen ‘yan jam’iyyun adawa ne da ake tsammanin Tinubu zai yi aiki da su a gwamnatinsa.

Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso babban dan siyasa ne kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata, yana daya daga cikin wadanda ake sa ran za su iya shiga gwamnatin Tinubu a dama dasu.

Kara karanta wannan

Murnar APC ta koma ciki: Atiku ya kada hanjin Tinubu, zai kawo shaidu 100 gaban kotu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso a kwanan nan ya tabbatar da haduwarsu da Tinubu a kasar Faransa yayin da ya bayyana zagewarsa don yin aiki da sabuwar gwamnatin.

Nyesom Wike

Yana daya daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP wanda ake tsammanin zai yi aiki da Tinubu a sabuwar gwamnati da za a kafa a 29 ga watan Mayu.

A lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar, Wike ya yi iyakar bakin kokarinsa don ganin Tinubu da APC sun ci jihar Rivers, kuma ya cika burinsa na ganin ya salwantar da goben jam’iyyar PDP a jihar.

Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigo a jam’iyyar PDP yana daya daga cikin wadanda ba sa maganganun batanci ga Tinubu.

Ana sa ran Tinubu zai iya aiki da shi a sabuwar gwamnatin da za a kafa a wannan wata, ganin yadda jiga-jigan jam’iyyar PDP suka juyawa dan takararsu Atiku Abubakar baya.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

Chimaroke Nnamami Nnamani

Tsohon gwamnan jihar Enugu ne kuma Sanata har na tsawon wa’adi biyu a majalisar dattawa da ya wakilci Enugu ta Gabas.

A lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar, Nnamani ya fito fili ya goyi bayan Tinubu wanda hakan ya yi sanadin korarsa a jam’iyyar ta PDP.

Daga baya ya yi takarar sanata in da ya rasa kujerar ga dan takarar jam’iyyar Labour.

Reno Omokri

Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kuma jigo a yakin neman zaben Atiku, a baya-bayan nan ya yabi halayen zababben shugaban kasa Tinubu.

A martanin da ya yi wa Peter Obi kan maganarsa da yace mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fi cancanta akan Tinubu, Omokri ya ce Tinubu ya fi Obi da Osinbajo cancanta sau goma.

Lamidi Apapa

Shugaban zagin jam’iyyar Labour a kwanan nan an zargi cewa Bola Tinubu da jam’iyyar APC suke daukar nauyinsa don kawo cikas a karar da aka shigar akan korafe-korafen zabe.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Amurka Tayi wa Najeriya da Sakataren Gwamnati Ya Kira Tinubu a Waya

Duk da cewa Apapa ya musanta zargin da ake masa na cewa ana daukar nauyinsa, amma ya tabbatar cewa idan Tinubu ya gayyace shi zai amsa gayyatar.

Atiku zai gabatar da shaidun da za su rusa Tinubu

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya ce yana da shaidu 100 da zai gabatar a gaban kotu.

Ya bayyana hakan ne ta bakin lauyansa a zaman da aka yi yau a gaban kotun raba gardamar zabe da aka zauna.

A baya, Atiku ya ce bai amince Tinubu ya yi nasara a zaben bana ba, don haka a tabbatar da ba a rantsar dashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel