Abinda Ya Sa Gwamna Matawalle Ba Zai Maida Martani Kan Tuhumar EFCC Ba

Abinda Ya Sa Gwamna Matawalle Ba Zai Maida Martani Kan Tuhumar EFCC Ba

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ba zai ce komai ba a yanzu game da zargin da EFCC ke masa
  • Mai magana da yawun gwamnan, Zailani Bappa, ne ya bayyana haka ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, 2023
  • Hukumar EFCC tana binciken Matawalle bisa zargin karkatar da wasu kuɗi biliyan N70bn da ya karbo bashi daga banki

Zamfara - Kakakin gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce mai gidansa ba zai ce komai game da zargin da hukumar EFCC ta masa na karkatar wasu kuɗi biliyan N70bn ba a halin yanzu.

Premium Times ta rahoto cewa da safiyar Alhamis, hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) tace tana binciken Matawalle bisa zargin karkatar da wasu kuɗaɗe.

Bello Matawalle.
Abinda Ya Sa Gwamna Matawalle Ba Zai Maida Martani Kan Tuhumar EFCC Ba Hoto: Bello Matawalle
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust ya nuna Matawalle ya sauya wa kuɗin akala ne bayan ya karɓo su da sunan bashi daga wani Banki da nufin gudanar da muhimman ayyuka a kananan hukumomin Zamfara.

Kara karanta wannan

An Fara Musayar Yawu Tsakanin Gwamnatin Buhari da Gwamnan APC Kan Satar Kuɗin Talakawa

Meyasa Matawalle bai maida martani kan batun ba?

Yayin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun gwamna Matawalle, Zailani Bappa, ya ce mai girma gwamna yana kan shirye-shiryen sauka daga gadon mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan ya ƙara da cewa gwamna Matawalle ba zai maida martani kan zargin da EFCC take masa ba yanzu domin hankalinsa na kan nauyin da al'umma suka ɗora masa.

Bappa ya ce:

"Nan da ƙasa da mako biyu mai girma gwamna zai sauka daga kan mulki, saboda haka banga dalilin da zai sa mai girma gwamna ya tsaya yana maida martani kan zargin da EFCC ke masa ba."

Bappa ya ce yana kan nazari kan tuhumar da EFCC take wa uban gidansa amma a matsayinta na hukuma ta tarayya, tana da ikon zargin duk wanda ya yi ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC Na Binciken Gwamna Matawalle Na Zamfara Kan Badakalar N70bn

Gwamna Matawalle na da sauran kwanaki 10 kacal a kan kujerar mulki kuma da zaran ya sauka doka zata sabule rigar kariyar da ke jikinsa.

Ku Jira Hukuncin Kotu Kafin Halatta Nasarar Bola Tinuhu, Obi Ga Amurka

A wani labarin kuma Peter Obi Ya Ɗau Zafi, Ya Maida Martani Ga Amurka Kan Kiran Bola Tinubu Ta Waya.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a zaben da ya wuce ya ce ya kamata Amurka ta dakata zuwa lokacin da Kotun zaɓe a Najeriya zata yanke hukunci gabanin ta halatta nasarar Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel