Ku Jira Hukuncin Kotu Kafin Halatta Nasarar Bola Tinuhu, Obi Ga Amurka

Ku Jira Hukuncin Kotu Kafin Halatta Nasarar Bola Tinuhu, Obi Ga Amurka

  • Ɗan takarar LP a zaben shugaban ƙasan 2023, Peter Obi, ya buƙaci Amurka ta jira har sai Kotun zaɓe ta yanke hukunci
  • Obi ya faɗi haka ne yayin martani ga kiran da sakataren Amurka, Antony Blinken, ya yi wa Bola Tinubu ta wayar tarho
  • A cewar Obi, ya kamata Amurka ta ƙara hakurin jira gabanin ta halatta nasarar zababben shugaban ƙasa

Ɗan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a inuwar Labour Party, Peter Obi, ya maida martani kan kiran da sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya yi wa Bola Tinubu ta wayar tarho.

Obi ya ce har yanzun babu cikakken bayani kan ainihin abinda Blinken da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, suka tattauna ta wayar tarho.

Peter Obi.
Ku Jira Hukuncin Kotu Kafin Halatta Masarar Bola Tinuhu, Obi Ga Amurka Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

A wasu jerin rubutun martani kan batun da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Jumu'a 19 ga watan Mayu, 2023, Obi ya ce ya kamata Amurka ta dakata, kar ta yi riga malam Masallaci.

Kara karanta wannan

Muhimman Abu 2 da Suka Jawo Allah Ya Hana Atiku da Peter Obi Mulkin Najeriya a 2023

A cewar Mista Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya kamata ƙasar Amurka ta jira zuwa lokacin da Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa zata yanke hukunci kafin halatta zaben Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Peter Obi ya wallafa cewa:

"Har yanzun babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa Sakataren wajen Amurka, Antony Blinken, ya kira ɗan takarar shugaban kasa inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu ta wayar tarho ranar 16 ga watan Mayu, 2023."
"Abinda ya fi komai muhimmanci da ƙima a tsarin Demokuraɗiyya shi ne kundin dokoki."

Idan baku manta ba, ranar Talata da ta gabata, Sakataren Amurka, Antony Blinken, ya kira shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ta wayar salula.

Rahoto ya nuna cewa Blinken ya jaddada shirin Amurka na kara yauƙaka dangantakar da ke tsakaninta da Najeriya a zamanin mulkin sabon shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Shugaba Buhari Ya Sanar da Muhimmin Abu 1 da Zai Wa Tinubu da Shettima Kafin Ya Sauka

Ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ake sa ran Tinubu zai shiga Ofis bayan wa'adin shugaba Muhammadu Buhari, ya ƙare.

Abinda Ya Janyo Atiku da Peter Obi Suka Sha Kashi a Zaben 2023, Shittu

A wani rahoton na daban kun ji cewa Jigon APC ya jero Muhimman Abu 2 da Suka Jawo Allah Ya Hana Atiku da Peter Obi Mulkin Najeriya a 2023.

Adebayo Shittu, ya ce idan mutane suka kwatanta kuri'un APC a 2019 da 2023, zasu gane cewa da Atiku da Obi sun haɗa kai, da yanzu ba wannan labarin ake ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel