Zargin Almundahana: "Kana da Yancin Faɗar Ra'ayinka," FG Ta Maida Martani Ga Matawalle

Zargin Almundahana: "Kana da Yancin Faɗar Ra'ayinka," FG Ta Maida Martani Ga Matawalle

  • Gwamnatin Buhari ta maida martani ga kalaman gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, na jam'iyyar APC
  • Matawalle ya buƙaci hukumar EFCC ta fara binciken Ministoci da wasu yan cikin fadar shugaban kasa
  • Ministan yada labarai da al'adu, Lai Muhammed, ya ce gwamnan na da yancin faɗar ra'ayinsa ko ya ba da shawara

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yana da damar da kowa ke da ita ta yancin faɗin albarkacin baki da ra'ayinsa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

FG ta ce wannan dama Matawalle ya yi amfani da ita yayin da ya ce ya kamata hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta fara bincikar Ministocin Buhari.

Bello Matawalle da Lai.
Zargin Almundahana: "Kana da Yancin Faɗar Ra'ayinka," FG Ta Maida Martani Ga Matawalle Hoto: Bello Matawalle, Daily Trust
Asali: Facebook

Sakon da Matawalle ya aike wa EFCC

Gwamna Matawalle ya ƙalubalanci shugaban EFCC na ƙasa, Abdulrasheed Bawa, ya fara bibiyar Ministoci da sauran mambobin majalisar zartaswa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Gwamnonin Arewa Na APC Sun Bayyana Matsaya Kan Shugabancin Majalisa Ta 10

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, maimakon maida hankali kan gwamnoni kamata ya yi a ga Bawa da tawagarsa sun fara dirar mikiya fadar shugaban ƙasa da kuma kan mambobin majalisar zartaswa (FEC).

Matawalle ya kuma roki shugaban EFCC ya tabbata duk wani bincike da hukumarsa zata sa a gaba ya shafi kowa ba wai a zaɓi wasu 'yan kalilan da aka raina ba.

"Ina buƙatar shugaban EFCC ya aika sammaci ga wasu jami'ai a fadar shugaban ƙasa da Ministoci, waɗanda ke cikin gwamnati lamba ɗaya a ƙasar nan," inji Matawalle.

FG Ta maida martani

Yayin maida martani, gwamnatin tarayya ta bakin Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ce gwamnan ya faɗi ra'ayin kansa ne kawai.

Channels tv ta ce sa'ilin da aka nemi ya yi martani kan kalaman Matawalle, Ministan ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: EFCC Na Binciken Gwamna Matawalle Na Zamfara Kan Badakalar N70bn

"Mai girma gwamna yana da damar ba da shawara, wannan ra'ayinsa ne."

Buhari zai karrama Tinubu da Shettima

A wani labarin kuma kun ji cewa Buhari Zai Karrama Tinubu da Shettima da Lambar Yabo Ta Kasa Gabanin Rantsarwa a hukumance.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Buhari zai karrama zababben shugaban ƙasa da mataimakinsa ranar 25 ga watan Mayu, 2023, kwana 4 kafin wa'adinsa ya cika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel