Jam’iyyar PDP Ta Karrama Gwamnonin PDP, Ciki Har da Gwamna Wiki da Wasu 2 Na G-5

Jam’iyyar PDP Ta Karrama Gwamnonin PDP, Ciki Har da Gwamna Wiki da Wasu 2 Na G-5

  • Gwamna Nyesom Wike da ‘yan tawagarsa na gwamnonin G-5 sun karbi lambar yabo daga jam’iyyar PDP
  • Jam’iyyar PDP ta ba gwamna Wike na Ribas lambar yabo ne tare da Samuel Ortom na Benue da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu
  • A bangare guda, kunsan yadda Wike da ‘yan tawagarsa na G-5 suka bayyana adawarsu ga dan takarar shugaban kasan PDP, Alhaji Atiku Abubakar

FCT, Abuja - Majalisar gwamnonin jam’iyyar PDP ta ba gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas lambar yabo bisa daukar muradin jam’iyyar, kasa da al’umma fiye da nasa.

Majalisar ta ba da wannan lambar yabon ne yayin da jam’iyyar ke tarbar zababbun gwamnoninta a wani bikin da aka gudanar a Abuja.

Idan baku manta ba, gwamna Wike na daya daga cikin gwamnonin da suka yi tasiri wajen faduwar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa da ya wakana.

Kara karanta wannan

Goro a Miya: Wasu Shugabannin APC Sun Kebe da Makiyin Tinubu, Tsohon Shugaba a PDP

Jam'iyyar PDP ta karrama jiga-jiganta
Gwamnonin G-5 'yan adawa da kiyayya ga Atiku | Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

PDP ta ba gwamnonin G-5 lambobin yabo

Samuel Ortom na jihar Benue da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu na daga cikin wadanda suka samu wannan yabo a jam’iyyar PDP, rahoton TheCable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a yayin bikin, Aminu Tambuwar, gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban majalisar, ya yaba wa takwarorin nasa bisa ba da hadin kai da dagewa tare da sanya muradan jam’iyyar a gaba.

Baya ga wadannan gwamnoni, an kuma ba wasu manya kuma jiga-jigan jam’iyyar lambobin yabo bisa ba jam’iyya gudunmawa.

Sauran wadanda aka ba lambobin yabo

Sauran wadanda aka ba lambobin yabo sun hada da tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko, tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose da Ibrahim Dankwambo, tsohon gwamnan Gombe.

Hakazalika, akwai tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Serieke Dickson daga cikin wadannan jiga-jigan da suka samu yabon jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Haka kuma, dukkan sabbin gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar PDP sun samu lambobin yabo don karfafa musu gwiwa don ciyar da jam’iyyar gaba.

Atiku ya cancanci yabo bisa ba APC damar nasara a zaben bana, inji Kayode

A wani labarin, kunji yadda jigon APC ya bayyana irin alherin da Atiku ya yiwa APC wajen samun nasara a zaben bana.

Femi Fani Kayode ya bayyana cewa, Atiku ya yi aiki yadda jam’iyyarsa ta PDP ta gaza nasara, inda Bola Tinubu ya ci zabe.

Wannan batu na zuwa ne daidai lokacin da dan siyasar ke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel