Ziyarar Tinubu: An Yi Zargin Abu 1 da Wike da Zababben Shugaban Kasa Suka Kulla a Ribas

Ziyarar Tinubu: An Yi Zargin Abu 1 da Wike da Zababben Shugaban Kasa Suka Kulla a Ribas

  • Ana tsammanin zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya baiwa gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sabon aiki
  • Bayanai sun nuna cewa wannan ci gaban ya biyo bayan ziyarar da Tinubu ya kai jihar Ribas da sunan kaddamar da ayyuka
  • Ƙungiyar CRPA ta yi ikirarin cewa Wike ya karbi aikin karya ƙarfin ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar gaban Kotun zabe

An fara tunanin cewa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyara jihar ne ba don kaddamar da ayyukan gwamna Nyesom Wike kaɗai ba, akwai wata a ƙasa.

A wata sanarwa da ƙungiyar 'The Centre for Reform and Public Advocacy (CRPA),' ta ce tana zargin akwai wani kulli da jiga-jigan siyasar biyu suka yi yayin wanan ziyara.

Tinubu, Wike da Atiku.
Ziyarar Tinubu: An Yi Zargin Abu 1 da Wike da Zababben Shugaban Kasa Suka Kulla a Ribas Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A sanarwan wacce ta shiga hannun Legit.ng Hausa, ƙungiyar ta yi ikirarin cewa babbar ajendar Tinubu ita ce ya nemi taimakon Wike domin ya shiga ya rage karsashin karar da jam'iyyun adawa suka shigar Kotu.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Dalili 1 Rak da Yasa Tinubu da APC Suka Zabi Akpabio da Abbas, Shettima Ya Tona Gaskiya

Tsagin adawa, wanda ya kunshi jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, Labour Party da Peter Obi, sun garzaya Kotun zaɓe, sun kalulanci matakin INEC na ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar CRPA, Ifeanyi Okechukwu, ya ce an ɗora gwamna Wike kan wannan aikin ne saboda yadda ya ƙosa ya shiga cikin muƙarraban gwamnatin Tinubu.

Okechukwu ya ce:

"Tunda ta bayyana karara Wike ya ƙosa ya samu muƙami a gwamnatin zababben shugaban ƙasa, hakan ya sa aka ɗora shi kan aikin ruguza ƙarar da jam'iyyarsa da LP suka ƙalubalanci nasarar APC."
"Duk da APC ba ta tabbacin ko zai yi aikin amma ba don komai Wike ya gayyato shugaba mai jiran gado ya kaddamar da ginin Kotu a Ribas ba sai don ya gamsar da shi cewa yana da gogewar aiwatar da duk aikin da aka ɗora masa."

Kara karanta wannan

"Allah Ne Ya Cece Mu" Gwamna Arewa Ya Tona Ainihin Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Goyi Bayan Tinubu

Matar Wike zata taka muhimmiyar rawa

An tattaro cewa mai ɗakin Wike kuma mace ta farko a jihar Ribas, Mai shari'a Eberechi Suzzette Wike, zata taka muhimmiyar rawa a wannan aikin.

Okechukwu ya kara da cewa gayyato Tinubu wani shiri ne na samun damar da tawagar zababben shugaban ƙasan ta gana da gwamna Wike da nufin cimma matsaya.

Dalilin da Yasa Muka Zabi Akpabio a Abbas a Matsayin Shugabannin Majalisa, Shettima

A wani labarin kuma Zababben Mataimakin Shugaban Kasa Ya Tona Asalin Dalilin da Yasa Suka Zabi Akpabio da Abbas a Majalisa Ta 10

A cewar Kashim Shettima, suna kokarin samar da daidaiton addini domin gudun tsoma APC a cikin masu yunkurin maida Najeriya ƙasar Musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel