Ana Tsaka da Dambarwar Yahaya Bello, Hukumar EFCC Ta Yi Garambawul a Mukamai

Ana Tsaka da Dambarwar Yahaya Bello, Hukumar EFCC Ta Yi Garambawul a Mukamai

  • Yayin da ya ke ta kokarin kawo karshen cin hanci da rashawa, shugaban EFCC ya yi garambawul a hukumar da sabbin nade-nade
  • Ola Olukoyede ya nada sabon shugaban ma'aikatansa da kuma wasu sabbin darektocin yankuna 14 a fadin ƙasar
  • Hakan ya zo a dai-dai lokacin da hukumar ke cikin dambarwa da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello kan badakalar N84bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya yi sabbin nade-nade a hukumar.

Olukoyede ya amince da sabbin darektoci 14 a yankuna domin tabbatar da inganta ayyukan hukumar da kuma sauke nauyin da aka daura musu.

Hukumar EFCC ta yi garambawul ana tsaka da neman Yahaya Bello
Shugaba hukumar EFCC ya yi sabbin nade-nade domin daura damar yaki da cin hanci. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: UGC

Waye aka nada shugaban ma'aikatan EFCC?

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Kotu ta umarci shugaban EFCC ya gurfana a gabanta, ta jero dalilai

Har ila yau, shugaban hukumar ya nada Michael Nzekwe a matsayin shugaban ma'aikatansa, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nzekwe ya kasance kwararren lauya wanda kuma shi ne tsohon kwamandan yanki na hukumar da ke birnin Ilorin a jihar Kwara.

Sakataren yada labaran hukumar, Dele Oyewale shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 27 ga watan Afrilu, cewar Punch

Olukoyede ya daga darajar ofisoshin yankin inda ya nada darekta a kowane bangare domin tabbatar yin aiki tukuru a kokarin yaki da cin bana.

An kuma kirkiri wani sabon ofishi a karkashin shugaban hukumar wanda tsohon kwamandan yanki a Makurdi, Friday Ebelo zai jagoranta.

Musabbabin yin sabbin nade-nade a EFCC

"Nzekwe kwararren mai gudanarwa ne wanda ya halarci kwasa-kwasai da dama a gida da kuma kasashen ketare."
"Dukkan nade-naden za su fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba."

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

"Olukoyede ya ce wannan garambawul din an yi ne saboda inganta ayyukan hukumar a kokarin dakile matsalar cin hanci a Najeriya."

- Dele Oyewale

Kotu ta bada sabon umarni ga shugaban EFCC

A wani labarin, kun ji cewa wata babbar kotu a jihar Kogi ta umarci shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya gurfana a gabanta.

Kotu ta ba shugaban hukumar kwanaki inda ta ce dole ya hallara kan zargin saɓa umarninta a binciken tsohon gwamna jihar, Yahaya Bello.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke tuhumar tsohon gwamnan kan badakalar N84bn lokacin da ya ke mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel