Dakarun Soji Sun Ceto Ma'aikatan Jin Kai da Yan Ta'adda Suka Sace a Borno

Dakarun Soji Sun Ceto Ma'aikatan Jin Kai da Yan Ta'adda Suka Sace a Borno

  • Jami'an rundunar Sojin Najeriya sun ceto ma'aikatan kungiyar NG0 biyu da yan ta'adda suka sace a Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa har yanzun ragowar ma'aikaci ɗaya da masu gadi biyu na hannun mayaƙan ISWAP
  • Hukumar sojin Najeriya da kungiyar da ma'aikatan ke wa aiki ba su ce komai ba tun lokacin da labarin sace su ya fito

Borno - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar ceto ma'aikatan jin ƙai 2 daga cikin 3, waɗanda ke aiki da Family Health International (FHI360) a jihar Borno.

Majiyoyi daga jami'an tsaro da mazauna yankin sun tabbatar da samun wannan nasara ga jaridar Daily Trust ranar Alhamis 4 ga watan Mayu, 2023.

Nasarar Sojoji a Borno.
Dakarun Soji Sun Ceto Ma'aikatan Jin Kai da Yan Ta'adda Suka Sace a Borno Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ma'aikatan da ke aikin taimaka wa al'umma sun shaƙi iskar yanci sanadiyyar Sojin Najeriya bayan mayaƙan kungiyar ta'addanci ISWAP sun yi garkuwa da su kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kwamishinam Zaben Jihar Adamawa Ya Shiga Komar Yan Sanda, Bayanai Sun Fito

Idan baku manta ba, yan ta'addan sun yi awon gaba da ma'aikata uku da masu gadi biyu a gidan baƙi na kungiyar ta ƙasa da ƙasa da ke ƙauyen Fotoko, kusa da garin Gamborou Ngala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta bayyana cewa biyu daga cikin ma'aikatan NGO uku sun shaƙi iskar yanci ranar Laraba amma ragowar ɗaya da kuma masu gadi biyu na hannun 'yan ta'adda.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar sojin Najeriya ko kungiyar NGO tun lokacin da aka sace ma'aikatan.

Borno na fama da ayyukan ta'addanci daga mayaƙan Boko Haram da kuma ƙungiyar da ta balle daga ciki watau ISWAP, kamar yadda Ripples Nigeria ta rahoto.

A baya yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi a Borno amma yanzun sojoji da sauran hukumomin tsaro sun kwato su.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

Ɗaya daga cikin alkawurran da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa yan Najeriya gabanin hawa mulki a 2015 shi ne gwamnatinsa zata murƙushe Boko Haram.

Yan bindiga sun kashe ASP a Abiya

A wani labarin kuma kun ji cewa Yan Bindiga Sun Gutsire Kan Babban Jami'in Hukumar Yan Sanda a Jihar Abiya

Marigayi ɗan sandan wanda ya kai muƙamin mataimakin sufurtandan yan sanda (ASP) ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ja tawagarsa zuwa wurin binciken ababen hawa.

Har kawo yanzun hukumar yan sanda ba ta ce komai ba a hukumance amma wani jami'i ya ce sun fara bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel