Miyagu Sun Tare Hanya Cikin Dare, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Miyagu Sun Tare Hanya Cikin Dare, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

  • Miyagun ɓata gari sun tare wasu matafiya akan hanya sun yi awon gaba da su, a jihar Edo
  • Masu garkuwa da mutanen dai sun yi kwanton ɓauna ne, inda suka sace fasinjoji sama da mutum 12
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta ce tana jiran samun cikakken rahoto ne kafin tace komai akan lamarin

Jihar Edo - Sama da mutum 12 ciki har da wata ƙaramar yarinya ƴar shekara 12 aka sace a kan titin hanyar Auchi-Ihievbe-Afuze, wacce ta haɗa ƙananan hukumomin Etsako West da Owan East na jihar Edo.

An dai yi awon gaba da matafiyan ne da misalin ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe 7 na daren ranar Talata.

Yan bindiga sun sace matafiya a jihar Edo
Taswirar jihar Edo Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard tace ko a jiya da aka tuntubi kakakin rundunar ƴa sandan jihar Chidi Nwabuzor, ya bayyana cewa suna jiran cikakken rahoto ne daga wajen DPO na yankin, kafin su ce wani abu kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yadda Kasar Masar Ta Umarci Ɗaliban Najeriya Sama da 500 Su Koma Sudan Kan Halayyar Mutum 2

Sai dai wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce mutum 9 aka sace sannan mutum 2 sun samu nasarar guduwa ba a sace su ba. Wani bidiyo ya nuna wasu motoci uku da aka bari a bakin titi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin motocin ƙirar Mercedes ML 320 Jeep mai AGD 542 GU wacce ba kowa a cikinta sannan ƙofofin ta na buɗe, ɗayar kuma ƙirar Toyota Sienna mai lamba Kogi LKJ 464 YE, yayin da mota ta ukun ba ta fito ba sosai, wacce a cewar mai ɗaukar bidiyon, mutanen cikinta sun gudu.

Muryar namijin da ke ɗaukar bidiyon, ya ce ƴan sakai a yankin sun bazama cikin dajin Warrake da sauran ƙauyuka domin ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace.

An samo cewa mutanen da lamarin ya ritsa da su, ciki har da ƙaramar yarinya mai shekara 9, an sace su ne a cikin motar Sienna.

Kara karanta wannan

Bayan Kwashe Kwanaki a Hannun 'Yan Sanda, An Bayar Da Belin Yunusa-Ari, An Gindaya Masa Sharudda

"Kwanton ɓauna aka yi wa fasinjojin inda wasu daga cikin su, ciki har da wata mace sun samu sun gudu amma ba ta samu ta ɗauki ɗiyarta ba wacce za ta kai shekara 9." A cewar muryar.

Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Hukumar Yan Sanda a Jihar Anambra

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun mamayi wasu jami'an ƴan sanda da ke a kan bakin aikin su, inda suka halaka wasu daga cikin su.

Ƴan bindigan dai sun buɗewa ƴan sandan wuta ne a lokacin da cike bakin aikin su, a wajen shingen bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel