Naɗin Sarki Charles: Bola Tinubu Ya Aika Wasika Ta Musamman Ga Sabon Sarkin Ingila

Naɗin Sarki Charles: Bola Tinubu Ya Aika Wasika Ta Musamman Ga Sabon Sarkin Ingila

  • Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tura wasiƙar taya murna ga Sarki Charles na III
  • Tinubu ya yi fatan nan gaba ya haɗu da sabon Sarkin, wanda aka naɗa shi a hukumance ranar Asabar 6 ga watan Mayu
  • Sarki Charles na III ya gaji wurin da babu kamarsa a tarihi, ya zama Sarki na farko da aka naɗa a Birtaniya tun 1937

FCT, Abuja - Zababben shugaban ƙasa a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wasiƙar taya murna ga Sarki Charles na III biyo bayan naɗinsa ranar Asabar 6 ga watan Mayu.

A wasiƙar wacce Legit.ng Hausa ta gani, Tinubu ya isar ga gaisuwa da sakon taya murna ga Sarki Charles III kuma ya yi fatan kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Burtaniya zata ƙara danƙo a zamanin mulkin Sarkin.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Malamin Addini Ya Hango Gagarumar Matsala a Kawancen Tinubu Da Gwamnan PDP

Tinubu da Sarki Charles III
Naɗin Sarki Charles: Bola Tinubu Ya Aika Wasika Ta Musamman Ga Sabon Sarkin Ingila Hoto: Olukayode Jaiyeola
Asali: Getty Images

Zababben shugaban kasan ya yaba wa sabon Sarkin Ingila bisa juriya da fahimtar al'adu mabanbanta kana ya roki ya ci gaba da haka cikin lura da yanayin mutane a Nahiyar Afirka da sauran ƙasashen duniya.

Tinubu ya yi fatan haɗuwa da ganawa da Sarkin Ingila nan gaba

Tinubu ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya fara aiki da Sarki Charles III, wanda hakan zai ba shi damar zama da Sarkin nan ba da jimawa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A karshen wasiƙar, Bola Tinubu, ya kara taya Sarki Charles III murnar naɗin da aka masa kana ya yi Addu'ar Allah ya ba shi kwarin guiwar sauke nauyin da aka ɗora masa cikin nasara a tsawon zamanin mulkinsa.

Shugaba mai jiran gado ya ce nasarar Sarkin ba al'ummar Birtaniya kaɗai zata amfana ba, baki ɗaya duniya zasu amfana.

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

Nan da mako uku da kwana biyu, ranar 29 ga watan Mayu, 2023, za'a rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya. Zai gaji shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban PDP Na Kasa, Iyorchia Ayu, Na Dab da Sanin Makomarsa a Kotu

A wani labarin kuma Babbar Kotun jihar Benuwai ta shirya yanke hukunci kan dambarwar tsige shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa.

Iyorchia Ayu, ya sauka daga mukaminsa bisa umarnin Kotun jihar Benuwai da ke zama a Makurdi bayan gundumarsa ta dakatar da shi.

A karshen makon nan, Kotun ta sanya ranar 26 ga watan Mayu, 2023 domin yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar gabanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel