Shugaban PDP Na Kasa, Iyorchia Ayu, Na Dab da Sanin Makomarsa a Kotu

Shugaban PDP Na Kasa, Iyorchia Ayu, Na Dab da Sanin Makomarsa a Kotu

  • Babbar Kotun jihar Benuwai zata yanke hukuncin kan ƙarar da shigar da shugaban PDP na ƙasa ranar 26 ga watan Mayu
  • Dakta Iyorchia Ayu, ya sauka daga shugabancin PDP bayan umarnin Kotu, yana jiran sanin makomarsa
  • PDP na fama da rikicin cikin gida tun kafin babban zaben 2023 kuma rigimar ta fi zafi kan kujerar shugaban jam'iyya

Benue - Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, wanda ya sauka bisa umarnin Kotu, na dab da sanin hukuncin da babban Kotun Makurɗi zata yanke a kansa.

Kotun karkashin jagorancin shugaban Alƙalan jihar Benuwai, Mai Shari'a Maurice Ikpambese, ta zabi ranar 26 ga watan Mayu, domin yanke hukunci kan ƙarar neman tsige Ayu daga shugabancin PDP.

Iyorchia Ayu.
Shugaban PDP Na Kasa, Iyorchia Ayu, Na Dab da Sanin Makomarsa a Kotu Hoto: PDP
Asali: UGC

Tun farko wani jigon PDP a jihar Banuwai, Conrad Utaan, ya maka Ayu a gaban Kotu bayan kwamitin zartaswa na gundumar Igyorov ya dakatar da shi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikicin Jam'iyyar Adawa Ya Kara Tsanani, Ta Dakatar da Manyan Jiga-Jigai 3

Yadda zaman Kotu ya gudana a karshen mako

Yayin da aka dawo sauraron ƙarar a karshen makon nan, lauyan Dakta Ayu, Yakubu Maikasuwa (SAN), ya kalubalanci karar da cewa kotu ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jam'iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ƙara da cewa wanda ya shigar da ƙara, "Ya yi fatali da duk wata hanyar da aka bullo domin yin sulhu tun a cikin gida ba tare da zuwa gaban Ƙotu ba."

Lauyan ya yi bayanin cewa, "Babu wani abu na kuskure da aka yi wa wanda ya shigar da ƙarar kuma babu wani abun amfani ko ƙima da zai samu daga wannan shari'a."

Da yake maida martani lauyan mai shigar da ƙara, Emmanual Ukala (SAN), ya ce batutuwan ba na cikin gida bane, kuma Kotu na ikon sauraro domin ba yau aka fara ba.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Obi? Tsohon Shugaban Kasa Ya Roki Alfarma 1 Wurin Yan Najeriya Kan Shari'ar Zaben 2023

Ya kafa hujja da hukuncin babbar Kotun Ribas kan tsohon shugaban PDP, Uche Secondus, da hukuncin Kotun ɗaukaka kara kan ƙarar tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole.

Ranar yanke hukunci

Bayan sauraron kowane ɓangare, mai shari'a Ikpambese ya ɗage zaman zuwa ranar 26 ga watan Mayu, 2023 domin yanke hukunci.

A wani labarin kuma Rikicin Jam'iyyar Adawa Ya Kara Tsanani, Ta Dakatar da Manyan Jiga-Jigai 3

Rigingimun cikin gida a jam'iyyar adawa watau Labour Party (LP) ya kara daukar zafi bayan darewar jam'iyyar zuwa gida biyu.

LP reshen jihar Kaduna ta ce ba ruwanta da tsagin Lamidi Apapa, wanda ke ayyana kansa a shugaban LP na ƙasa. Haka nan ta dakatar da manyan kusoshi 3, cikin har da yan takara a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel