Akwai Matsala: Malamin Addini Ya Hango Gagarumar Matsala a Kawancen Tinubu Da Gwamnan PDP

Akwai Matsala: Malamin Addini Ya Hango Gagarumar Matsala a Kawancen Tinubu Da Gwamnan PDP

  • Wani babban malamin addini ya hango cewa dangantakar da ke tsakanin gwamna Wike sa Bola Tinubu ba mai ɗorewa ba ce
  • Primate Ayodole ya bayyana cewa na kusa da Tinubu dole za su yaƙi gwamna Wike bayan an yi rantsuwa
  • Babban faston ya kuma hango wata gagarumar rigima da za ta taso a jam'iyyar APC da zarar an rantsar da Tinubu

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi iƙirarin cewa ɗasawar da ake yanzu tsakanin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ba za ta yi ƙarko ba.

Jaridar Vanguard tace Primate Ayodele ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin sa Oluwatosin Osho, ya fitar.

Babban fasto ya hango Tinubu da Wike za su bata
Bola Tinubu da Nyesom Wike a wajen taro Hoto: PresElectNgr
Asali: Twitter

Kalamansa na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya ziyarci jihar Rivers domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Wike ta yi a jihar.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Tare Hanya Cikin Dare, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

A cewar malamin addinin, na kurkusa da gwamnatin APC mai zuwa, ba za su shirya da Wike ba, cewar rahoton Daily Post.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa sai an sanya gwamnan ya yi cizon yatsa kan abubuwan da ya riƙa yi yanzu.

Babban faston ya yi nuni da cewa, bayan an rantsar da gwamnatin Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, abubuwa da dama za su sauya.

Ya kuma ƙara da cewa waɗanda ke jiran samu muƙamai masu gwaɓi, na iya tashi a tutar babu, saboda rabon muƙamai zai kawo ruɗani sosai a jam'iyyar.

A kalamansa:

"Ɗasawar da Wike ya ke yi da APC ba za ta daɗe ba. Ƴan gaban goshi a gwamnatin za su yaƙe shi, sannan sai ya ciza yatsa sosai, amma ba zai gane hakan ba yanzu. APC za ta koya masa darasi da sauran ƴan PDP da suka sauya sheƙa."

Kara karanta wannan

Lauyoyi 50 Za Su Kare Nasarar Cin Zaben Shugaban Kasa Na Tinubu: Sunayen Manya 17 Daga Cikinsu Ya Fito

"Bayan an yi rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayu, abubuwa da dama za su sauya. Waɗanda suka yi tsammanin samun kaso mai tsoka na iya tashi a tutar babu. Rabon muƙamai zai kawo rikici a APC bayan an yi rantsuwa."

Ana Dab Da Rantsar Da Shi, Bola Tinubu Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sha wani muhimmin alwashi ga ƴan Najeriya.

Shugaban ƙasan mai jiran gado ya bayyana cewa dukkanin wasu alƙawura da ya ɗauka zai cika su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel