Gwamnatin Buhari Zata Tura Ƙarin Jiragen Sama Su Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan

Gwamnatin Buhari Zata Tura Ƙarin Jiragen Sama Su Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan

  • Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta ce FG ta tura ƙarin jiragen sama zuwa Masar domin ɗebo yan Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan rukunin farko da ya kunshi mutane 376 sun diro Najeriya daga Masar bayan guje wa yakin Sudan
  • Ta kuma bayyana halin da ake ciki dangane da kwaso yan Najeriyan da ke jibge a bakin ruwan Sudan

Abuja - Shugabar hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da cewa ƙarin jiragen sama sun nufi Masar domin kwaso yan Najeriyan da suka tsere daga Sudan.

Dabiri-Erewa ta ba da wannan tabbacin ne a filin jirgin Nnamdi Azikwe, Abuja yayin da ta karbi rukunin farko da suka iso Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Aikin jigilar yan Najeriya.
Gwamnatin Buhari Zata Tura Ƙarin Jiragen Sama Su Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Ta ce akalla dai sun dawo gida kuma abun farin ciki babu wanda ya mutu a can sannan kuma gwamnati ta fi ba da fifiko ga dalibai, mata da kananan yara, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Jami'in Ɗan Sanda Ta Wani Yanayi Mai Ban Tausayi

A kalamanta, ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Saboda haka bisa shirin da NEMA ta yi, muna tsammanin za'a samu ƙarin jiragen da zasu yi aikin jigilar saboda ƙasar Masar ta kafa sharaɗi mai wahala."
"Masar ta ce idan adadin mutanen da suka shiga ƙasarsa 200 ne misali, kuma jirgin da muka tura yana cin 150 ne, to ba wanda zamu ɗauka."
"Bukatarsu ku kwashe dukkan mutanen da kuka kawo a lokaci ɗaya. Idan jiragen sama huɗu suka dira lokaci guda to zamu kwaso yan uwanmu baki ɗaya. Don haka NEMA ta tabbatar da cika sharaɗin Masar."

Wane hali yan Najeriya suke ciki a bakin ruwan Sudan?

Bugu da ƙari, Dabiri-Erewa ta ce shirye-shirye sun yi nisa a kokarin kwaso 'yan Najeriyan da suka isa bakin gabar ruwan Sudan.

A cewar shugabar NiDCOM, batun yan Najeriya da suka isa bakin ruwan Sudan ya banbanta saboda yana da wuya Jirgin sama ya sauka a yankin wurin.

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: Jiragen da Suka Kwaso 'Yan Najeriya Sun Taso Daga Masar, An Samu Matsala

"A tashar jirgin ruwan Sudan, muna kokarin samun tikitin jirgi saboda abu ne mai wuya jirgin sama ya sauka a bakin ruwan amma su na da kamfanin jirgi, a halin yanzu muna bin matakan da ya dace."
"Mun saya musu tikitin tafiya daga nan kuma zasu taho zuwa gida kuma da zaran jiragen mu sun samu izinin sauka, zasu tafi da hanzari."

Yan Najeriya da Suka Tsere Daga Rikicin Sudan Sun Taso Daga Masar a Jirgi

A wani labarin kuma Jiragen da Suka Kwaso 'Yan Najeriya Sun Taso Daga Masar, Amma An Samu Matsala

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan Najeriyan da suka gudo daga Sudan suka shiga Masar, sun taso daga Filin jirgi zuwa gida Najeriya.

Sai ɗai gabanin tasowarsu an samu wata yar matsala wajen cika sharaɗin kasar Masar na kwashe kowa da kowa a lokaci ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel