"Mun Ga Ta Kan Mu", Daliban Da Aka Kwaso Daga Sudan Sun Bayyana Halin Kuncin Da Suka Tsinci kan Su a Ciki

"Mun Ga Ta Kan Mu", Daliban Da Aka Kwaso Daga Sudan Sun Bayyana Halin Kuncin Da Suka Tsinci kan Su a Ciki

  • Wasu daga cikin ƴan Najeriyan da suka samu dawowa daga Sudan, sun yi ƙarin haske kan ƙuncin da suka shiga
  • Ɗaliban sun bayyana cewa sun shiga matsi wanda har ya kai wasu daga ciki, suna bin hanyoyin tsira da ran su
  • Wasu daga cikin su, sun yi zargin cewa an ci zarafin mata daga cikin su a bakin iyakar Masar da Sudan

Abuja - Ɗalibai ƴan Najeriya da suka dawo gida daga ƙasar Masar, sun bayyana halin ƙuncin da suka tsinci kan su a ciki, inda wasu suka yi zargin cewa an ci zarafin wasu mata daga cikin su.

Halin ƙunci da matsin da suka tsinci kan su a ciki, ya kai ga komai na su ya ƙare wanda har ya tilasta wasu daga cikin yin ƴan ɗauke-ɗauke a shaguna suna ran ta ana kare, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Cafke Wani Basarake Mai Hada Baki Da 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya

Yan Najeriya sun bayyana kuncin da suka shiga a Sudan
Wasu daga cikin 'yan Najeriya da suka dawo gida a cikin jirgi Hoto: Air Peace
Source: Twitter

Wata ɗaliba wacce ta dawo ta gayawa ƴan jarida a filin jirgin sama na Abuja, cewa sun fuskanci cin mutunci sannan har a filin Allah ta'ala sun kwana. Ɗalibar dai tana magana ne akan halin da suka tsinci kan su a bakin iyakar Sudan da Masar.

A kalamanta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun ƙarar da duk ƴan kuɗaɗen da mu ke da su. Mun ji yunwa da ƙishirwa sosai. Har cin zarafin mu suke yi. Babu abinci, babu ruwan sha. Har ya kai jallin da sai da mu ka yi ɗan hali a shaguna mu ka tsere."

Wata ɗaliba ta bayyana cewa ƙafafun su har kumbura suka yi saboda tsawon lokacin da suka kwashe suna tafiya cikin motoci.

Da yake magana kan halin da ya shiga, wani ɗalibi ya bayyana cewa lamarin ya yi munin da sai sun biya kuɗi kafin a bari su yi fitsari, cewar rahoton Parrot Nigeria.

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: Jiragen da Suka Kwaso 'Yan Najeriya Sun Taso Daga Masar, An Samu Matsala

Ɗalibin ya yi fatan cewa yaƙin ya zo ƙarshe cikin gaggawa domin ya samu damar komawa Sudan, ya kammala karatun sa wanda ya rage saura zango ɗaya kawai ya kammala.

Allah Ya yi, Saitin Farkon ‘Yan Najeriya 350 da Yaki Ya Rutsa da su a Sudan Sun Dawo

Da zu mu ka kawo rahoto, kan yadda jirgin farko ɗauke da ƴan Najeriyan da rikicin Sudan ya ritsa da su, suka dawo gida Najeriya.

Sahun farko da ya samu isowa gida Najeriya, yana ɗauke ne da mutum 350.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng