Yan Najeriya da Suka Tsere Daga Rikicin Sudan Sun Taso Daga Masar a Jirgi

Yan Najeriya da Suka Tsere Daga Rikicin Sudan Sun Taso Daga Masar a Jirgi

  • Ɗaliban Najeriya da suka tsira daga yakin da ya barke a Sudan sun taso daga Filin jirgin ƙasar Masar zuwa Najeriya
  • Sai dai gabanin tasowar jiragen da suka kwaso su, sharadin da Masar ta kafa ya jawo tsaikon lokacin tashi
  • Masar ta kafa sharadin cewa dole Najeriya ta kwashe mutanenta lokaci ɗaya ba tare an bar ko mutum ɗaya ba

'Yan Najeriyan da aka kwaso domin guje wa yaƙin da ya kaure a ƙasar Sudan, sun taso daga filin jiragen saman Aswan na ƙasar Masar.

Da farko jirgin rundunar sojin saman Najeriya mai lamba NAF C130 da kuma jirgin kamfanin Air Peace mai ɗaukar fasinjoji 274, sun tsara tasowa da misalin ƙarfe 1:00 agogon Najeriya amma hakan ba ta samu ba.

Daliban Najeriya.
Yan Najeriya da Suka Tsere Daga Rikicin Sudan Sun Taso Daga Masar a Jirgi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Hukumomin ƙasar Masar sun tsaya kan bakarsu cewa wajibi Najeriya ta kwashe baki ɗaya mutanenta da suka shigo ƙasar daga Sudan a lokaci guda.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jiragen Yaƙi 2 Sun Kai Hari Kan Fadar Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito

Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa Masar ta sahalewa yan Najeriyan shiga filin jiragen sama tsakanin jiya da daddare da kuma safiyar yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar da aka samu tun farko

Majiyar ta ce:

"Aƙalla fasinjoji 25 aka karawa jirgin sojin sama bayan adadin fasinja 80 da yake ɗauka, domin kawai a cika sharaɗin gwamnatin Masar amma duk da haka wasu ba su samu wuri ba, shiyasa aka ɗaga tafiyar da farko."
"Matuƙin jirgin NAF ya aminta zai kwashe su baki ɗaya amma bisa sharaɗin banda kayansu. Don haka jami'an gwamnati suka nemi shawarin iyaye, sun amince da cewa rayuwar yayansu ta fi muhimmanci."
"Amma duk da haka kalilan daga cikinsu suka kafe kai da fata dole su tafi da kayansu waɗanda ke tattare da takardun karatu."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa daga karshe jirgin rundunar sojin sama ya kwashe ragowar fasinjojin amma ban da kayayyakinsu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Manyan Malamai Uku Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Halin da ake ciki a jigilar yan Najeriya daga Sudan

A wani labarin kuma Kun ji cewa Daliban Najeriya Da Motarsu Ta Kama Da Wuta Sun Isa Tashar Jirgin Ruwan Sudan

A rukuni na biyu a aikin jigilar yan Najeriya daga Sudan, wasu ɗalibai sun gamu da matsala a hanyarsu ta zuwa tashar jirgin ruwan Sudan.

Ɗaya ɗaga cikin motocin Bas ɗin da ta kwaso yan Najeriya ta kama da wuta a shingen RSF, lamarin da ya sa dole wasu suka kwana a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel