Sojoji Sun Cafke Wani Basarake Mai Hada Baki Da 'Yan Bindiga a Kaduna

Sojoji Sun Cafke Wani Basarake Mai Hada Baki Da 'Yan Bindiga a Kaduna

  • Dakarun sojoji sun kai sumame a wani ƙauye cikin jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu da ake zargi da haɗa baki da ƴan bindiga
  • Madakin Janjala, cikin ƙaramar hukumar Kagarko, na daga cikin waɗanda sojojin suka tafi da su
  • Ana zargin su da haɗa baki da ƴan bindiga waɗanda suka ɗade suna satar mutane a yankin

Jihar Kaduna - Sojoji sun kai sumame a ƙauyen Janjala cikin ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, inda suka cafke Madakin Janjala, Mallam Ibrahim Aliyu, da wasu mutum 13 masu ba ƴan bindiga bayanai.

Wani majiya wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya gayawa jaridar Daily Trust cewa, sojojin sun shigo garin ne ranar Talata akan motoci 8 ƙirar Hilux, da babura sannan suka tafi da waɗanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Rikicin Sudan: Jiragen da Suka Kwaso 'Yan Najeriya Sun Taso Daga Masar, An Samu Matsala

Sojoji sun cafke basarake mai hada baki da 'yan bindiga a Kaduna
Dakarun sojoji Hoto: RipplesNigeria.com
Asali: UGC

Ya ce sojojin sai da suka tsaya a Kagarko inda nan suka cafke wasu da ake zargi, kafin su ƙaraso zuwa ƙauyen Janjala, wanda ke da nisan kilomita 3 daga Kagarko.

"Mutum biyun da ake zargi da aka kama a Kagarko sun yi wa sojojin jagora zuwa wasu gidaje a Janjala, inda suka ƙara cafke wasu mutum 11." A cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin Janjala mai suna, Yahuza Suleiman, ya bayyana cewa sojojin sun tafi da Madakin garin zuwa Kaduna, saboda sace-sacen mutane da ake yi a ƙauyen.

"Sannan tun sanda sojoji suka tafi da Madaki da wasu waɗanda ake zargi, lambar wayar sa ba ta tafiya, amma wani wanda na samu na yi magana da shi yau da safe, ya gaya min cewa yana can yana amsa tambayoyi a Kaduna, kan sace-sacen mutanen da ake yi a Janjala." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Manyan Malamai Uku Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Ƴan bindiga dai sun daɗe suna addabar ƙauyen Janjala da ƙauyukan da ke makwabtaka da shi, inda suke sace mutane da halaka wasu daga cikin su.

Yan Bindiga Sun Gutsire Kan Babban Jami'in Yan Sanda

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun halaka wani babban jami'in ɗan sanda a jihar Abia, ta wata mummunar hanya.

Ƴan bindigan dai sun halaka jami'in ɗan sandan ne ta hanyar guntile masa, cikin rashin imani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel