Allah Ya yi, Saitin Farkon ‘Yan Najeriya 350 da Yaki Ya Rutsa da su a Sudan Sun Dawo

Allah Ya yi, Saitin Farkon ‘Yan Najeriya 350 da Yaki Ya Rutsa da su a Sudan Sun Dawo

  • Dalibai da sauran mutanen da aka dauko daga Sudan sun sauka Abuja da ƙarfe 11:30 na dare
  • Jiragen farko na Air Peace da na sojoji sun dura filin jiragen saman Nnamdi Azikwe a Abuja
  • Wadannan mutane sun biyo ta filin kasar Masar ne bayan sun tsallaka iyakokin Sudan da kyar

Abuja - Sahun farko na mutanen Najeriya da aka kubutar daga yakin kasar Sudan sun yi nasarar shigowa kasarsu bayan an dauki lokaci ana fama.

Rahoton da BBC Hausa ta fitar ya tabbatar da wadannan Bayin Allah sun sauka a filin tashin jirgin Nnamdi Azikiwe bayan dare ya tsala a ranar Laraba.

An dauko ‘Yan Najeriyan ne a jirgin sojojin ruwan kasar da wani jirgi da shugaban kamfanin Air Peace, Mista Allen Onyema ya bada a dalilin hakan.

Kara karanta wannan

“Tukunyar ‘Non-Stick Mai Bakin Ciki Na Iya Haifar Da Cuta”: Likita Ya Shawarci Jama’a Kan Amfani Da Tukunyar Zamani Wajen Girki

Yayin da jirgin sojojin ya dauko mutane 94, mutane 283 su ka shigo jirgin Air Peace, da kimanin karfe 11:30 na dare dukkansu su ka iso garin Abuja.

Ana wulakanta 'Yan Najeriya

This Day ta ce Shugaban kamfanin jirgin Air Peace, Allen Onyema ya zargi Sudan da nunawa ‘Yan Najeriya bambanci ba tare da sun yi wani laifi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ji Onyema yana mai zargin kasashen Afrika da yin kudi da Najeriya saboda yakin.

Jirgi
Jirgin Air Peace da ya dauko 'Yan Sudan Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Godiyar Sadiya Umar-Farouq

Ministar bada agajin gagagwa da jin-kai a Najeriya, Sadiya Umar-Farouq ta shaidawa manema labarai cewa kusan mutane 350 aka dauko a sahun farko.

A cewar Sadiya Farouq, akwai mutane fiye da 1, 000 da suka rage da za a dauko nan gaba.

Jiragen saman za su koma domin su cigaba da dauko mutane daga kasar. A jawabinta, Ministar ta godewa shugaban kasa, Air Peace da jami’ai.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cika Hannu Da Yan Sara-Suka 98 a Wata Jihar Arewa

Shugabar hukumar NIDCOM mai kula da ‘yan ci-rani, Abike Dabiri-Erewa ta ji dadin ganin mutanen kasarta bayan irin wahalar da suka sha a hanya.

Ana sauraron zuwansu

Wadannan mutane sun shigo Najeriya ne bayan sun baro Sudan, sun biyo ta Masar a jiya. Hukumomin Masar sun ce ba za a bar masu mutum ko daya ba.

Tun yammacin Laraba, hukumomin Najeriya su ka tabbatar da cewa ‘yan kasarta sun yi nasarar barin Sudan inda ake yaki, sun tsallaka iyakar Masar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel