Yan Bindiga Sun Gutsire Kan Babban Jami'in Yan Sanda a Jihar Abiya

Yan Bindiga Sun Gutsire Kan Babban Jami'in Yan Sanda a Jihar Abiya

  • Tsagerun yan bindiga sun halaka babban jami'i a hukumar yan sanda yayin da ya fita aikin bincike a jihar Abiya
  • Rahoto ya nuna cewa ɗan sandan wanda ya kai matsayin ASP, yana shirin aje aiki a watan Satumba mai zuwa
  • Wata majiya daga cikin hukumar yan sanda reshen Abiya ta ce tuni aka fara bincike don damƙo maharan

Abia - Miyagun 'yan bindiga sun kashe mataimakin Sufuritandan yan sanda (ASP) wanda ke aiki a hukumar 'yan sanda ta jihar Abiya, daga bisani suka fille masa kai.

The Nation ta tattaro cewa marigayi ASP wanda aka gano sunansa “Agbalagba” a takaice, yana aiki ne a Caji Ofis din Ndiegoro da ke ƙaramar hukumar Aba ta kudu a jihar Abia.

Yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Gutsire Kan Babban Jami'in Yan Sanda a Jihar Abiya Hoto: thenationonline
Asali: Twitter

Rahoton da jaridar ta tattara ya nuna cewa yan bindigan, bayan sheke ɗan sandan da kuma raba kansa da gangar jikinsa, sun yi awon gaba da bindigarsa ta aiki da Kakin 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Yi Wa Wasu Matasa Biyu Yankan Rago a Jihar Filato

Marigayi ASP, ɗan asalin jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya, wanda ke jagorantar tawagar sintiri, yana dab da yin ritaya daga aiki a watan Satumba mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ce marigayi Agbalagba da yan tawagarsa sun fita aikin binciken ababen hawa da sanyin safiyar Talata a Titin Kamaru daga kuiɓin gabas, ba zato ba tsammanin yan bindigan suka far musu.

Wane mataki hukumar 'yan sanda ta ɗauka?

Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda reshen jihar Abiya, Geoffrey Ogbonna, bai ɗaga kiran waya ko amsa sakkonnin da aka tura masa kan lamarin ba.

Amma wata majiya a rundunar yan sanda ta tabbatar kisan mataimakin Sufuritandan, inda ta ƙara da cewa tuni aka fara bincike don zakulo duk masu hannu.

Jihar Abiya na cikin jihohin da suke fama da hare-haren yan bindiga waɗanda ake zargin mayaƙan kungiyar ta'addanci IPOB ne, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shekau, Anini, Oyenusi Da Wasu Yan Ta'adda 2 Da Suka Addabi Najeriya

Rasha ta zargi Ukraine da yunkurin kashe Putin

A wani labarin kuma Jiragen Yaki Marasa Matuka Sun Kai Hari Fadar Shugaban Kasar Rasha

Ƙasar Rasha ta zargi Ukraine da yunkurin kai hari fadar shugaban ƙasa Putin ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa guda biyu.

Gwamnatin Ukraine ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa ta maida martani kan wannan zargi da aka rataya mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel