Wasu Malamai Uku da Karin Mutum Daya Sun Mutu a Hadarin Mota a Ekiti

Wasu Malamai Uku da Karin Mutum Daya Sun Mutu a Hadarin Mota a Ekiti

  • Wani hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4 a jihar Ekiti, cikinsu har da Malaman Coci uku da yammacin Litinin
  • Wata majiya ta ce Malaman suna hanyar zuwa sabon cocin da aka tura ɗayansu lokacin da ibtila'in ya afka masu
  • Kakakin 'yan sanda a jihar, DSP Abutu ya tababatar da faruwat haɗarin, ya ce suna kan bincike

Ekiti - Mutum huɗu, waɗanda suka ƙunshi Malaman Addinin Kirista guda 3 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da rutsa da su a jihar Ekiti.

Leadership ta rahoto cewa hatsarin ya afku ne da yammacin ranar Litinin a kan Titin Otun–Iro Ekiti, ƙaramar hukumar Moba a jihar da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Baya ga waɗanda suka rasa rayuwarsu, wasu mutum biyar sun ji raunuka kala daban-daban a haɗarin motar.

Kara karanta wannan

Shugaban Hukumar Tsaro a Jihar Arewa Ya Tsallake Rijiya Da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Cikakkun Bayanai Sun Bayyana

Hadarin mota.
Wasu Malamai Uku da Karin Mutum Daya Sun Mutu a Hadarin Mota a Ekiti Hoto: leadership
Asali: UGC

Wasu majiyoyi sun shaida wa yan jarida a Ado-Ekiti, babban birnin jihar cewa Mamatan sun taso daga Ipere-Ekiti zuwa Iro-Ekiti lokacin da Ibtila'in ya afka kan motarsu, kuma nan take rai ya yi halinsa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran waɗanda suka ji raunuka na kwance a Asibitin koyarwa na tarayya da ke Ado Ekiti, suna karɓan magani yayin da gawarwakin waɗanda suka mutu aka aje su a ɗakin ajiyar gawa.

Su waye Malaman da haɗarin ya rutsa da su?

Bayanai sun nuna cewa ɗaya daga cikin Malaman ya samu canjin wurin aiki daga Cocin Ipere Ekiti kuma sauran Malaman biyu sun rako abokinsu zuwa sabon cocin da aka maida shi a Iro-Ekiti sa'ilin da suka gamu da ajalinsu.

An ce sauran Malaman biyu suna wa'azi ne a cocin da kowanensu ke jagoranta a garuruwan Eda Oniyo da kuma Ewu Ekiti.

Kara karanta wannan

Shiri Ya Lalace: Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Malaman Addini Cikin Tsakar Dare

Wata mata, wacce take da alaƙar yan uwantaka da marigayi Faston da aka sauya wa wurin Wa'azi, tana cikin waɗanda suka mutu a haɗarin.

Wane mataki 'yan sanda suka ɗauka?

Yayin da aka tuntube shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Ekiti, DSP Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Jaridar Punch ta rahoto Abutu yana cewa:

"Mun samu labari kuma mun tura jami'an yan sanda masu kula da harkokin hanya. Sun ɗauki gawar mamatan zuwa Asibiti inda aka tabbatar da rai ya yi halinsa."
"Muna kan nazari kan lamarin kuma bincike ya yi nisa don gano ainihin abinda ya haddasa hatsarin."

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Kwace Iko Da Majalisar Dokokin Jihar Abiya Kan Rigimar da Ta Barke

Sakamakon rikicin shugabancin da ya ɓarke, dakarun yan sanda sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Abiya.

Wasu yan majalisu sun ware kansu, kuma sun kaɗa kuri'ar tsige kakakin majalisar, hakan ya haddasa rabuwar kai.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Ɗaliban Jami'a a Najeriya, Rayuka Sun Salwanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel