Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Gini Ya Dane Ma'aikata a Abuja

Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Gini Ya Dane Ma'aikata a Abuja

  • Wata katanga ta danne masu aiki a kusa da wurin, ana fargabar mutum 2 sun kwanta dama yayin da wasu 4 ke kwance a Asibiti
  • Jami'an hukumar kai ɗaukin gaggawa ta birnin tarayya (FEMA) sun dira wurin da sauran hukumomin tsaro
  • Shugaban FEMA a Abuja, Idriss, ya ce sun samu kiran gaggawa a tsakanin karfe 10-11:00 na safe kan abinda ya faru

Abuja - Ana fargabar leburori biyu sun mutu a wurin wani gini da ake kan yi da ke yankin Ademola Adetokunbo Crescent, Wuse 2, a birnin tarayya Abuja yayin da wani shingen ginin ya rushe.

Daily Trust tace kawo yanzun an zaro ma'aikata huɗu da ransu yayin da wasu biyu kuma suka ji munanan raunuka ko motsi ba su yi, ana ci gaba da aikin ceto yanzu haka.

Kara karanta wannan

"Soyayya Ta Gaskiya": Yadda Bidiyon Wasu Ma'aurata Yan Unguwar Mallam Shehu Ya Ja Hankalin Masu Kallo Miliyan 1

Ginin Abuja.
Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Gini Ya Dane Ma'aikata a Abuja Hoto: thenation
Asali: UGC

Jami'an da ke aikin ceto a wurin sun haɗa da jami'an hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA), hukumar kai ɗaukin gaggawa ta birnin tarayya (FEMA), da dakarun Sibil defens.

Sauran sun da suka kai ɗauki don ceto waɗanda ginin ya rufta a kansu sun ƙunshi jami'an hukumar 'yan sanda da kuma mazauna yankin da suka sa kansu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daraktan FEMA, Dakta Abbas Idris, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga The Nation, ya ce mutum 4 da aka ciro da rai an tafi da su zuwa babban Asibitin Asokoro don musu magani.

An tattaro cewa ma'aikatan na kan aikin tona ramin kafa tushen wata katangar, matsin lambar sara ƙasa ne ya haddasa kifewar shingen ya murkushe biyu daga cikinsu.

Idriss ya ce:

"Hukumar FEMA ta amsa kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10-11:00 na safe cewa wani gini ya rushe a gefen bankin UBA, nan take muka haɗa dakaru suka nufi wurin."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Tashar Watsa Labarai a Najeriya Ta Kama Da Wuta a Watan Azumi

"Da isar jami'anmu suka gane katanga ce ta turmushe masu aiki a wurin. Yanzun mun ciro mutane 6, biyu sun ji muggan raunuka likita kaɗai zai tabbatar da mutuwarsu, hudu kuma na karɓan magani a Asibiti."

Gobara ta kama a gini mallakin gwamnatin Oyo

A wani labarin kuma Tashar Watsa Labarai Ta Gwamnatin Jihar Oyo Ta Kama Da Wuta

Babbar tashar watsa labarai mallakin gwamnati ta kama da wuta a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya. Wani ganau ya bayyana daga inda wutar ta fara kuma ta tafka ɓarna mai girma. A halin yanzun jami'an kwana-kwana sun duƙufa domin kashe wutar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel