Jami'in Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu a Hannun Yan Bindiga

Jami'in Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu a Hannun Yan Bindiga

  • A watan Azumin Ramadan, yan bindiga sun kashe wasu mutane da suka yi garkuwa da su a jihar Neja
  • Mai rijista a Kotun Musulunci da ke Ibbi, karamar hukumar Mashegu na ɗaya daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu
  • Wani mazauni ya ce yan ta'adda sun kashe mutanen yayin da jami'an tsaro suka matsa ƙaimi don ceto su

Niger - Rijistara mai kula da dukkanin bayanan harkokin Kotun shari'ar Musulunci da ke Ibbi, karamar hukumar Mashegu a jihar Neja, Mallam Namaru, ya rasu.

Daily Trust ta rahoto cewa 'yan bindiga ne suka kashe ma'aikacin Kotun Musuluncin mako biyu bayan sun yi garkuwa da shi a watan Ramadan.

Taswirar jihar Neja.
Jami'in Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu a Hannun Yan Bindiga Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da yasa suka kashe Mallam Namaru amma City & Crimeta tattaro cewa yan bindiga sun sace mamacin tare da wasu ranar 24 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Yan Fashi Da Makami Sun Kai Mummunan Hari Kasuwar Ogun Da Tsakar Rana, Sun Kashe Wani Dan Kasuwa

Duk wani yunkurin samun jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, kan batun kisan mutumin ya ci tura har kawo yanzu da muke haɗa rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa 'yan ta'addan suka kashe shi?

Amma wani mazaunin yankin, Abdullahi Abubakar, ya shaida wa wakilin jaridar cewa yan ta'addan sun bindige rijistaran da sauran waɗanda aka sace su tare saboda matsin lambar da suke sha daga jami'an tsaro.

Ya ce jami'an tsaro sun matsa kaimi don ceto mutanen shiyasa masu garkuwan suka halaka su. Ya ce sanadiyyar haka aka harbe wani ɗan banga har lahira.

Abubakar ya ce a halin yanzu ana ta kokarin ɗauko gawarwakin mutanen da aka kashe domin a musu Jana'iza da kuma ceto ragowar waɗanda ke raye

Mutumin yace garin Ibbi da ake ganin akwai zaman lafiya kuma har masu gudun Hijira ke samun mafaka, a mako biyu da suka shige ya fara fuskantar hare-hare.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari a Watan Azumi, Sun Kashe Mutane a Arewa

Yan bindiga Sun Kashe Mutane 9 A Kaduna

A wani labarin kun ji cewa wasu Yan bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace 20 a Sabon Harin Jihar Kaduna

An tattaro cewa maharan sun kuma kwace dabbobin jama'a, sun yi awon gaba da su bayan kashe rayuka 9 a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Wannan na zuwa ne awanni bayan dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar sheƙe wani shugaban 'yan bindiga, Isiya Ɗanwasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel