Yan bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace 20 a Sabon Harin Kaduna

Yan bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace 20 a Sabon Harin Kaduna

  • Yan bindiga sun yi ajalin mutane 9, sun sace wasu 20 a harin da suka kai kauyen Sabon Layi da ke jihar Kaduna
  • Bayanai sun nuna daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu a harin har da jami'an tsaron ƙungiyar yan banga
  • Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan rundunar Soji ta halaka babban shugaban yan binidga, Isiya Ɗanwasa

Kaduna - 'Yan bindiga sun halaka mutane 9, cikinsu har da jami'an tsaro na ƙungiyar Banga huɗu a ƙauyen Sabon Layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari, a jihar Kaduna.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan ta'addan masu yawa sun kutsa cikin ƙauyen kana suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi duk da ana cikin watan Azumi.

Yan bindiga.
Yan bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace 20 a Sabon Harin Kaduna Hoto: leadership
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa yayin wannan kazamin hari, yan bindigan sun yi ajalin mutane 9, kana daga bisani suka yi awon gaba da wasu 20 da dabbobin al'umma.

Kara karanta wannan

Jirgin Yaƙin Soji Ya Kai Ɗauki Yayin da Yan Bindiga Suka Kaiwa Mutane Hari da Azumi, Da Yawa Sun Mutu

Idan baku manta ba, bayan haɗa bayanan sirri, rundunar sojin operation Forest Sanity karkashin sashi na 1, sun kai samamen mamaya, suka sheke ƙasurgumin ɗan bindiga, Isiya Ɗanwasa, da mayaƙansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayanan sirrin da aka tattara tun farko sun nuna cewa shugaban 'yan bindigan ya yi nufin tura ɗaya daga ciki manyan yaransa mai suna Yunusa, ya siyo musu bindigu da Alburusai a garin Kaduna.

Mai magana da yawun sashi na 1 na rundunar sojin Najeriya, Laftanar Kanal Musa Yahaya, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce, "Daga nan aka bi diddigin yaron shugaban 'yan bindigan har sojoji a cikin fararen kaya suka ɗauko shi kuma suka yi amfani da shi wajen jawo manyan yan ta'adda wani wurin siyar da Alburusai."

A cewar Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Ɗanwasa ke ɗaukar nauyin kai harin kashe-kashe, garkuwa da mutane da satar dabbobi.

Kara karanta wannan

A Watan Ramadan, Wani Mutumi Ya Kutsa Kai, Ya Caka Wa Liman Wuka Ana Tskaa da Sallar Asuba

Ɗan ta'addan ya sheƙa barzahu a hannun sojojin yayin wani samamen kwantan bauta a garin Sabon Birni da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi.

Jirgin Sojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga a Birnin Gwari

A wani labarin kuma Jirgin yakin sojojin Najeriya ya sheƙe yan bindiga da dama yayin da suka yi yunkurin tserewa a Kaduna

Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, ya ce rundunar sojin saman ta gaggauta kai ɗauki ne bayan samun kira daga yankin Birnin Gwari cewa yan bindiga sun shiga ƙauye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel