Yan Fashi Sun Farmaki Kasuwar Ogun, Sun Kashe Wani Dan Kasuwa

Yan Fashi Sun Farmaki Kasuwar Ogun, Sun Kashe Wani Dan Kasuwa

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki jama'a a kasuwar wayoyi da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun
  • Maharan da suka kai mamaya kasuwar da tsakar ranar Laraba sun kashe wani dan kasuwa
  • Jami'an tsaro sun yi nasarar cafke mutum daya a cikin yan fashin inda suka kaddamar da bincike a kansa

Ogun - Wasu da ake zaton masu fashi da makami ne sun farmaki shahararriyar kasuwar wayoyi da kayan wuta da aka fi sani da 'Computer Village' a Abeokuta, jihar Ogun inda suka kashe wani dan kasuwa.

Yan bindigar da yawansu ya kai takwas sun farmaki kasuwar da ke Oke-Ilewo, Abeokuta, da tsakar ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu don aiwatar da aika-aikarsu, Daily Trust ta rahoto.

Shaidu sun ce maharan na ta harbe-harbe, lamarin da ya haddasa tashin hankali tsakanin yan kasuwa inda suka tarwatse don neman mafika.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Harbe Sufeton Dan Sanda Da Ke Hutu Da Iyalinsa

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yan Fashi Sun Farmaki Kasuwar Ogun, Sun Kashe Wani Dan Kasuwa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sai dai kuma, wasu shaidu sun kuma yi zargin cewa yan bindigar na iya kasance mambobin kungiyar asiri da ke bibiyan abokan hamayyarsu ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa wasu matasa masu ciniki a kasuwar sun dakile harin daga bisani inda suka kama mutum daya.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, cewa yan sandan sun yi nasarar dakile fashin.

Oyeyemi ya fada ma manema labarai cewa:

"Guggun yan fashin sun farmaki kasuwar da misalin karfe 5:30 na yamma, suka fara harbi kan mai uwa da wahabi sannan suka sace tsadaddun wayoyi."

Ya bayyana cewa an yi wani kira mai cike da damuwa ofishin yan sandan Ibara sannan DPO na yankin, CSP Abayomi Adeniji, ya gaggauta tura yan sandan yaki da fashi da makami tare da tawagar hadin gwiwa na Amotekun zuwa wajen.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Sojoji Sun Murkushe Kasurgumin Dan Bindigar Kaduna, Isiya Danwasa

A cewarsa, da hango yan sandan, yan bindigar sun yi musayar wuta da su amma saboda karfin wuta daga yan sandan, sai maharan suka ci na kare.

Ya bayyana Adeniji Sakiru mai shekaru 32 a matsayin wanda aka kama a yayin harin.

Oyeyemi ya ci gaba da cewa:

"Abun bakin ciki, wani Dayo Bankole, dan kasuwa a kasuwar, wanda yan fashin suka harba ya kwanta dama yayin da yake samun kulawar likitoci a babban asibitin Ijaye da ke Abeokuta."

Ya kuma bayyana cewa kwamishina mai barin gado, Frank Mba ya yi umurnin tura mai laifin da aka kama zuwa sashin binciken laifuka don ci gaba da bincike, rahoton The Cable.

Ya ce Mba, wanda ya kasance AIG a yanzu ya kuma yi umurnin kamo sauran masu laifin tare da gurfanar da su.

Ya roki asibitoci da su sanar da yan sanda idan suka ga wani da raunin harbi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga A Kano Sun Bi Dare Sun Sace Wani Fitaccen Dan Kasuwa, Sun Bindige Mutum 2

Yan bindiga sun sheke sufeton dan sanda a Imo

A wani labarin kuma, wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani sufeton dan sanda a Imo inda suka yi cikin jeji da shi. Bayan an kaddamar da bincike, an gano gawarsa a ciyashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel